logo

HAUSA

Cusa fasaha a zukatan yara

2021-01-06 19:21:16 CRI

Cusa fasaha a zukatan yara_fororder_下载

Yue Shi Tong, wata hukuma ce a birnin Qingdao na kasar Sin mai koyar da yara ilmin zane-zane. Ba kamar yadda sauran hukumomin fasaha suke mai da hankali kan sakamako ba, hukumar Yue Shitong ta fi mai da hankali kan ba da horo ga yara a fannin kwarewar fahimtar kyan abubuwa. Shugabar hukumar Mao Yanxin na ganin cewa, idan yara suka kware wajen fahimtar kyan abubuwa, to a lokacin za su koyi fasahar zane-zane cikin sauki. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani game da Mao Yanxin da ayyukan hukumar.

A shekarar 2015, Mao Yanxin ta yi murabus daga mukaminta na aikin malanta wanda ta shafe tsawon shekaru takwas tana koyarwa a birnin Beijing, daga baya kuma sai ta koma gida Qingdao don fara sana’a. Game da ra’ayin ta na fara sana’a, Mao Yanxin ta ce,

“Ina ganin, abin da ya fi muhimmanci a rayuwata shi ne, kare mutuncina. Na kuma gano cewa, abin da ya fi kwanta mini a rai shi ne, yin abubuwa tare da yara, ina sha’awar taimaka musu a lokacin da suke girma, sakamakon da na samu ya kan faranta min rai.”

Cusa fasaha a zukatan yara_fororder_8847a32cdadf4f89038d3c71d317c9bb

Mao Yanxin ta koyi fasahar koyar da yara ilmin zane-zane a yayin da take jami’a, daga baya kuma ta shafe shekaru 8 tana aikin malanta, don haka ta koyi wasu fasahohi a fannin koyar da yara ilmin zane-zane. Wannan ne kuma ya kasance dalilin da ya sa ta zabi fara sana’a da kanta, inda ta kafa wani dakin horas da yara a fannin zane-zane.  

“A lokacin, yawancin hukumomin koyar da ilmin zane-zane a birnin Qingdao sun fi mai da hankali ne kan yadda ake zane mai kyau kawai, idan an kalli irin zanen da yaran suka yi, za a gano cewa, e zane ne, amma ba shi da wani kyau. Ina fatan kyautata irin wannan, don haka, na tabbatar da manufar hukumarmu, wato mai da hankali kan fannin fahimtar kyan abubuwa, amma ba koyon fasaha kawai ba.”

Bayan ta tsaida kudurin raya sana’ar, sai ta yi hayar wani daki mai muraba’in mita 100, babu kayayyakin ado kuma ba a yi wani bikin bude dakin ba, sai kawai ta soma aikin koyarwa. Mao Yanxin ta bukaci dalibanta su kirata da malama Xiao Mao, a ganintam hakan na iya taimakawa wajen karfafa dangantakar dake tsakaninta da yaran. Bayan ta soma aikin koyarwa kuma, Mao Yanxin ta gamu da wasu matsaloli.  Ta ce,

“Babbar matsalar da ta fi damuna ita ce, sauya matsayi na daga wata malama dake koyarwa a makaranta zuwa mai raya sana’a, kuma ‘yar kasuwa. Mun fahimci aikin ilimi, da kuma ilimin halayyar yara, amma ba mu fahimci kasuwa ba. Daga baya, mun gano cewa, idan muna fatan gudanar da wani aiki yadda ya kamata bisa bukatun kasuwa, to, dole ne mu yi tsare-tsare kan kwasa kwasanmu, wato, mu tsara kwasa-kwasai daban daban bisa shekarun yara daban-daban, kuma kamata ya yi mu kafa hanyoyi daban daban wajen bayar da wadannan kwasa-kwasan. Ba ma son mu iyakance wani fannin da wai ya kamata yara su koya, a maimakon haka, muna fatan yara za su iya ganin kyan abubuwa ta fannoni daban-daban. Game da abubuwan da za su ba su sha'awa a nan gaba kuma, za su iya zabe da kansu, kuma su kara kokarinsu na kara kwarewa a wannan fanni."

Cusa fasaha a zukatan yara_fororder_b71b385131066a257e6637b7ed0a14b1

Daga farko dai, Mao Yanxin ba ta mayar da hankali kan raya hukumarta ba, a maimakon haka ta yi ta kokarin kara abubuwan dake cikin darussan da za a koyar da kuma karfafa matsayinta. Ban da darussan zane-zane da aka bullo da su na yau da kullum, ta kan kuma shirya ayyukan kai ziyara zuwa gidajan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi, don taimakawa yaran wajen kara matsayinsu na fahimtar kyan abubuwa ta hanyar ganin wadancan abubuwan fasaha na gargajiya.  

“A gani na, kamata ya yi mu baiwa yara wata dama ta sanin abubuwa da dama, a yayin da suke kanana za su iya haddace abubuwa da yawa, idan suka kara girma, abubuwan da suke koyo za su ragu, amma abubuwan na bukatar yara su kara mai da hankali a kai. A tunani na, kananan yara na bukatar sanin abubuwa da dama, bisa wannan ra’ayi ne na zabi bullo da darussan kai ziyara zuwa gidajen ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi. Bayan matsayinsu na fahimtar kyan abubuwa ya karu zuwa wani matsayi, hakan zai sa su koyi fasahar zane-zane da hannu cikin sauki. ”

Kafin darussan kai ziyara zuwa gidajen ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi, sai da Mao Yanxi ta gudanar da bincike a kai, don zabar wadanda suka fi dacewa da yara. Ta ce, ta fahimci yaranta sosai. Bisa kokarin da ta yi, yanzu akwai dalibai kusan 150 dake samun horo a hukumarta, wadanda suka fito daga wurare daban daban na birnin, kuma wasu daga cikinsu ma sun fito ne daga nesa.

Cusa fasaha a zukatan yara_fororder_bfb98fa85d888b930df8f9684da5adbe

Hukumar Yue Shitong na kara yin suna a wurin, hakan ya sa wasu gidajen renon yara su ma suka gayyaci Mao Yanxin don ta horar da malamai. Mao Yanxin ta ce,

“Wasu gidajen renon yara sun gayyace ni don na ba da darasi ga malamansu, kuma ina jin dadin fasahohin da yara suke koya. A matsayi tsohuwar malama, zuwa mai raya sana’a, kuma mai gudanar da harkoki, yanzu na sake koyon abubuwa a wajen wasu malamai, gaskiya matsayina ya sauya sosai, wannan ya ba ni kwarin gwiwa kwarai da gaske. ”

Mao Yanxin ta yi imanin cewa, duk kalubalolin da take fuskanta wajen raya sana’ar ta sun faru ne a kokarin neman kwarewa. Tana fatan kokarin da take yi zai taimakawa yara su samu ilmin fasahohi a hukumar Yue Shitong, za kuma su dauki fasaha a matsayin abin da ke cikin ransu, domin inganta rayuwarsu.