logo

HAUSA

Ziyarar da ministan harkokin wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon kowace shekara ta kasance tamkar wata kyakkyawar al’adar dake sada zumunta tsakanin Sin da Afirka

2021-01-06 09:00:00 CRI

Daga 4 zuwa 9 ga watan Janairun shekarar 2021 ne, dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Wang Yi, ya fara ziyarar aiki a kasashen Afirka 5, da suka hada da Najeriya, da Congo (Kinshasa), da Botswana, da Tanzania, da Seychelles.

Ziyarar da ministan harkokin wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon kowace shekara ta kasance tamkar wata kyakkyawar al’adar dake sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210106世界2021001-hoto1

Ziyarar tasa zuwa Afirka, ita ce ta farko da duk wani ministan wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon ko wace shekara, cikin shekaru 31 a jere, tun daga shekarar 1991.

Wannan ya kara tabbatar da cewa, kasar Sin sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa, baya ga shaida ci gaban kawance su, da hadin gwiwa mai wanzuwa, wanda ke tabbatar da karkon tsare tsaren diflomasiyyar Sin, da zabin ta na abokan hulda.

Ziyarar da ministan harkokin wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon kowace shekara ta kasance tamkar wata kyakkyawar al’adar dake sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210106世界2021001-hoto3

Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al'ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba.

Manufar wannan ziyara ita ce, sada zumunta, kuma dukkan sassan biyu suna goyon bayan juna, da ma yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da kara raya shawarar "ziri daya da hanya daya", kana suna martaba manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Ziyarar da ministan harkokin wajen Sin ke kaiwa ketare a duk farkon kowace shekara ta kasance tamkar wata kyakkyawar al’adar dake sada zumunta tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210106世界2021001-hoto2

Haka kuma, ministan zai yayata bukatar aiwatar da muhimman kudurori da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya cimma tare da shugabannin Afirka. Akwai kuma batun sakamakon taron kolin FOCAC na Beijing, taron musamman na hadin kan Sin da kasashen Afirka kan fannin yaki da COVID-19, da tallafi ga Afirka wajen yakar annobar, da cimma nasarar farfado da tattalin arziki, da fadada bukatar hada gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wajen aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da bunkasa gina al’umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da nahiyar Afirka.

Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarorin biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarorin gwamnatoci da al’ummomin sassan biyu. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)