logo

HAUSA

Yan siyasar Amurka masu neman moriyar kansu suna matukar damuwa

2021-01-06 20:54:40 CRI

Yan siyasar Amurka masu neman moriyar kansu suna matukar damuwa_fororder_1

A halin da ake ciki yanzu, a kasar Amurka, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya riga ya kai sama da miliyan 20, kuma adadin mutanen da suka rasu sakamakon annobar ya riga ya wuce dubu 350.

A Los Angeles na kasar kuwa, an tabbatar mutum guda na harbuwa da cutar a duk dakika 6. Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, annobar COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a kasar, har ta kai matsayin da ya zama abu mai babbar wahala a hana bazuwarta, amma duk da haka, wasu ‘yan siyasar Amurkan ba sa kula da wannan matsala, maimakon haka, suna yada bayanan karya domin dora laifi ga saura. Hakika dai suna cikin matukar damuwa.

Duk da cewa, kwanaki kasa da 20 kacal suka rage ga gwamnatin mai ci, amma ‘yan siyasar fadar White House ba su daina yin kokari kan manufar su ba. Alal misali, sun kasa kula da mawuyacin yanayin fama da yaduwar cutar COVID-19 da kasarsu ke ciki, suna yada sakamakon da suka ga dama. An lura cewa, a ranar 1 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya wallafa wani sako a dandalin sada zumunta na Twitter, mai taken “Amurka a yanzu ta fi Amurka kafin shekaru hudu da suka gabata tsaro”.

Yan siyasar Amurka masu neman moriyar kansu suna matukar damuwa_fororder_2

Kuma alal hakika mako guda kafin wannan rana, a duk dakika 33, Ba’amurke guda daya na mutu sakamakon cutar COVID-19. Abun tambaya a nan shi ne, ko wannan ce Amurkar da ta fi tsaro a idon ‘yan siyasar kasar? Ana iya cewa, suna yaudare kansu ne kawai.

Abun bakin ciki shi ne, al’ummun kasar Amurka wadanda ‘yan siyasar kasar suka kasa kula da su, suna cikin mawuyacin yanayi, bisa sabon hasashen da cibiyar tantance lafiyar jiki ta kwalejin koyar da ilmomin likitanci ta jami’ar Washington wato IHME a takaice ta fitar, an ce, a cikin wata mai zuwa, sabbin mutanen da za su mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a Amurka, za su kai dubu 115, lamarin da ya alamta cewa, al’ummun Amurka za su ci gaba da shan wahalhalun da annobar ke haifarwa.

Yan siyasar Amurka suna kokarin neman moriyar kansu, amma al’ummun kasar wadanda ba su ci ba ba su sha ba suna shan wahala, shin akwai yiyuwar kiran Amurka kasa mai ‘yancin kai? (Jamila)