logo

HAUSA

Kyakkyawar Jumma’a tun daga Laraba ake gane ta

2021-01-06 16:03:37 CRI

Kyakkyawar Jumma’a tun daga Laraba ake gane ta_fororder_0106

Yanzu haka ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yana ziyara a Najeriya, a ci gaba da rangadin aikin da yake a kasashen Afirka biyar, ziyarar dake zama al’ada ga duk wani ministan wajen Sin ke fara kaiwa a farkon kowace sabuwar shekara.

A lokacin da yake Najeriya, Wang Yi ya gana da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama, inda jami’an suka yi alkawarin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni.

A cikin sama da shekaru 50 da suka gabata, dangantakar Sin da Nijeriya ta haifar da muhimman sakamako. A matsayinsu na abokai na kwarai, lokacin da farashin mai ya fadi a kasuwar duniya, kuma Nijeriya take fuskantar matsalolin ci gaba, tallafin Sin ya taimaka mata, domin ta shawo kan matsalolin da suka hada da rashin kayayyakin more rayuwa da karancin abinci, abin da ke nuna, gagarumar rawar da Sin ta taka a fannin ci gaban Najeriyar. Matakin dake kara jaddada taimakon juna a kowane irin hali.

A matsayinta na babbar kasa a nahiyar Afrika, Nijeriya ta dauki wani muhimmin matsayi a bangaren dangantakar diflomasiyyar Sin da nahiyar Afrika. Kuma abu mafi muhimmanci a dangantakar kasashen biyu cikin shekaru 50 da kulla ta shi ne, fahimta da aminci da goyon bayan juna.

A don haka, ministan Wang ya kara jaddada aniyar Sin ta hada hannu da Nijeriya wajen daukaka huldar kasa da kasa da inganta tsarin demokuradiyya a dangantakar kasashen duniya da kare halaltattun hakkoki da muradun kasashen biyu da ma na sauran kasashe masu tasowa.

Kasashen biyu sun kuma amince, su ci gaba da karfafa hadin gwiwa a yaki da annobar COVID-19, da kara goyon bayan juna, har sai an ga bayan annobar baki daya, za kuma su kafa wani kwamiti tsakanin gwamnatocinsu karkashin kulawar ministocin wajen kasashen biyu, wanda zai tsara, da ma kara ciyar da hadin gwiwar moriyar juna a fannoni daban-daban.

Sin da Najeriya sun kuma bayyana kudirinsu na kara zurfafa hadin gwiwa, wajen bunkasa shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, ta hanyar hade sabon shirin raya na kasar Sin da sabon shirin raya kasa na Najeriya tare.

Daga karshe Wang ya ce, kasar Sin za ta kara gudanar da ayyukan samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a Najeriya, don taimaka mata hanzarta zamanantar da masana’antu da inganta karfinta na raya kasa. Don haka, duk wani makircin da wasu kasashen yamma ke yi na lahanta wannan dangantaka, ba za ta yi nasara ba. (Ibrahim Yaya)