Ana sa ran tattalin arzikin zamani da cinikayya ta yanar gizo za su zama sabbin abubuwan lura game da hadin gwiwar Sin da Afirka
2021-01-05 12:42:59 CRI
Tun daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Janairu, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai kai ziyarar aiki kasashen Najeriya, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Botswana, Tanzania, da Seychelles. Wannan al'ada ce ta ministan harkokin wajen kasar Sin ta zabar nahiyar Afirka a matsayin zangon farko na zayarasa a ketare a duk farkon ko wace shekara, tun daga shekarar 1991. Xu Jinghu, wakiliyar musamman ta gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka, ta fada a cikin wata hira ta musamman da CMG cewa, wannan ya nuna irin muhimmancin da kasar Sin ke baiwa ci gaban alakarta da Afirka.
Wakiliyar musamman ta gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka Xu Jinghu ta bayyana cewa, tun daga shekarar 1991, kasar Sin ba ta taba daina al’adarta ta ziyartar nahiyar Afirka ba, wadda ta kasance ziyara ta farko da duk wani ministan harkokin wajen kasar ke kaiwa ketare a duk farkon ko wace shekara. Babu wata kasa da za ta iya yin hakan kamar kasar Sin, wadda ke nuna cikakkiyar muhimmancin da Sin ke baiwa ci gaban dangantaka da Afirka. Madam Xu tana kuma ganin cewa, gina yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka zai taimaka matuka wajen zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Nan gaba, tattalin arzikin zamani da cinikayya ta yanar gizo, za su zama sabbin abubuwan lura na hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci. Ta ce,
“Musamman a wannan yanayin da ake ciki na fama da annobar COVID-19, dan majalisar gudanarwar kasa kuma ministan harkokin waje Wang Yi, yana ci gaba da wannan kyakkyawar al'adar, wato kamar a ko yaushe, ya zabi zuwa Afirka don ziyarar aiki ta farko a sabuwar shekara, wannan ya kara nuna sahihanci da kasar Sin ke da shi da kuma niyyarta ta bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Afirka, da kawance da 'yan uwantaka tsakanin bangarorin biyu, kuma wannan ma wani taimako ne mai karfi da Sin ta baiwa kasashen Afirka don yaki da annobar COVID-19 da samun farfadowar tattalin arziki. Mu kan ce, Sin da Afirka ko da yaushe, sun kasance al'umma da ke da makoma ta bai daya. A ganina, wannan ya tabbatar tare da bayyana kudurin kasar Sin na gina al’umma mai kyakkyawar makoma.”
Madam Xu Jinghu ta ce, a shekarar 2020, kawancen Sin da Afirka ya fuskanci kalubalen sabuwar annobar COVID-19, kuma ya kara samun ci gaba. Xu ta yi nuni da cewa, a mawuyacin lokacin da kasar Sin ta shiga sanadiyyar wannan annoba a farkon shekarar bara, abokai ‘yan Afirka sun ba ta gwarin gwiwa da goyon baya sosai. Dukkanin jami'ai, kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin shiyyar, kungiyoyin kawance da dai sauransu na kasashen da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin sun yi amfani da hanyoyi daban-daban don nuna cikakken goyon baya da kwarin gwiwa ga kasar Sin. Xu ta kara da cewa,
“Kasashen Afirka ba su da arziki, amma wasu kasashen ma sun ba da taimakon kudi da na kayayyaki ga kasar Sin. Wannan ya burge mu sosai. Bayan barkewar annobar a Afirka, mun shawo kan matsin da aka shiga a cikin gida na yaki da annobar, da kuma shawo kan matsaloli, ciki har da dakatar da zirga-zirga, mun samar wa kasashen Afirka da tarin kayan yaki da annobar cutar da sauran tallafi. Har ila yau, mun saukakawa kasashen Afirka sayen kayayyaki daga kasar Sin, tare da musayar fasahohin yaki da cutar da nahiyar, kana mun tura tawagogi da yawa na kwararrun likitocin zuwa kasashen Afirka. A watan Yunin shekarar 2020, Sin da Afirka sun gudanar da taron koli na musamman na yaki da annobar COVID-19 ta hanyar bidiyo, wannan shi ne taron koli daya tilo da aka yi tare da Afirka a tsakanin dukkan manyan kasashe.”
A ranar farko ta shekarar 2021, yankin cinikayya cikin ‘yanci na Afirka ya fara aiki a hukumance. Madam Xu ta yi nuni da cewa, kaddamar da yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka, zai rage shingen kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, da inganta musayar cinikayya tsakanin su, da hanzarta tsarin dunkulewar Afirka, da kara sakin damar da ke ciki na ci gaban Afirka. Ban da wannan kuma, zai kawo sabbin damammaki don kara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya.
“Misali, dangane da raya kayayyakin more rayuwa, wannan ya kasance wani muhimmin fanni da Sin da Afirka ke bawa muhimmanci. Gina yankin cinikayya cikin ‘yanci na bukatar kasashen Afirka su kara kyautata kayayyakin more rayuwa da kara hadewa da juna. Ina ganin hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu a wannan muhimmin fanni tabbas za ta kara karuwa.”
Shekarar 2021, shekara ce ta karshe ta aiwatar da sakamakon taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. Xu Jinghu ta ce, Sin da Afirka za su gudanar da taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a kasar Senegal a karshen rabin shekarar bana, inda za su tsara sabbin shirye-shirye kan hadin gwiwar bangarorin biyu, don himmantuwa da kara saurin sauye-sauye kan hadin gwiwar Sin da Afirka. (Bilkisu)