logo

HAUSA

Zumunta a kafa take

2021-01-05 18:10:35 CRI

Zumunta a kafa take_fororder_微信图片_20210105181010

Tun daga jiya Litinin, 4 ga watan nan na Junairu, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya fara ziyartar wasu kasashe 5 na nahiyar Afrika, da suka hada da Najeriya, da Congo (Kinshasa), da Botswana, da Tanzania, da Seychelles, ziyarar da zai kammala a ranar 9 ga wata. Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a kasashen Afrika a farkon kowacce shekara, ta zama wata kyakkyawar al’adar da ake ta daukaka ta tun daga shekarar 1991, wato shekaru 30 cif da suka gabata.

Kamar yadda ake cewa aminci da dangantakar Sin da Afrika daddadiya ce, tabbas wannan al’ada da ake ci gaba da rayawa, daya ce daga cikin shaidun dake tabbatar da hakan. Duk da yanayin da duniya ta tsinci kanta na fama da annobar COVID-19 mai yaduwa kamar wutar daji, Sin ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da wannan al’ada, tabbas wannan ya nuna abun da ake cewa, aboki na kwarai shi ne mai kasancewa da kai komai wuya komai rintsi.

Ziyarar ta Wang Yi a bana, ta zo a shekarar da za a kammala aiwatar da batutuwan da aka cimma yayin taron kolin Beijing, na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC da aka tsara aiwatarwa tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021. Ya kamata a ce wannan ziyara, ta share fagen tsara karin ayyuka, ko dorawa kan nasarorin da aka samu kan hadin gwiwar, wadanda suka shafi inganta dangantakarsu a fannonin cinikayya da samar da kayayyakin more rayuwa da musaya da kiwon lafiya da sauransu. Idan za a yi misali da ginin ababen more rayuwa da kasar Sin ke aiwatarwa a nahiyar Afrika, za a iya cewa ya dora nahiyar kan tafarkin samun ci gaba. A wannan gaba da aka fara amfani da yarjejeniyar yankin ciniki cikin ’yanci tsakanin kasashen nahiyar Afrika, hadin gwiwarsu da kasar Sin zai taka rawa matuka, a matsayinta na wadda ta ci gaba kuma mai gogewa. Gogewar kasar Sin zai zamarwa kasashen abun koyi da dogaro a fannin raya masana’antu da kuma samar da ababen more rayuwa da za su saukaka harkokin cinikayya da hade kasashen nahiyar kamar yadda suke fata.

Akwai kuma batun yaki da annobar COVID-19 da farfado da tattalin arziki daga halin da ya shiga sanadiyyar tasirin annobar. Abun nufi shi ne, zai yi kyau idan kasashen za su yi amfani da wannan dama ta ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin, su kara zurfafa hadin gwiwa da kasar, don ganowa tare da koyo dabarunta na yaki da cutar, ganin irin nasarar da ta samu a bangaren kawo yanzu. Sannan duk da tasirin annobar kan tattalin arzikin daukacin kasashen duniya, ta yi namijin kokari wajen zama kasa daya tilo da ta samu ci gaban tattalin arziki a bara. Don haka, hadin gwiwa da kasar Sin abu ne da ya zama wajibi domin ta kasance abar koyi kuma mai kaifin basira.

Ya kamata wannan ziyara ta kara tunatarwa kasashen Afrika da ma yammacin duniya cewa, Sin da gaske take dangane da zumunci da furuci da burinta na tallafawa kasashen Afrika. Duk da yadda harkokin rayuwa suka sauya a duniya a baya-bayan nan, Sin ta dage wajen daukaka zumuncin dake tsakaninta da ’yan uwanta na nahiyar Afrika, ta ci gaba da daukaka al’adarta da nufin karfafa dangantaka, lamarin da ya kuma haska yadda take daukar nahiyar Afrikar da al’ummominta da batutuwan da suka shafe ta da muhimmanci. (Faeza Mustapha)