logo

HAUSA

Abdullahi Tukur Bawa: Noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya na da makoma mai haske a Najeriya

2021-01-05 14:13:11 CRI

Abdullahi Tukur Bawa: Noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya na da makoma mai haske a Najeriya_fororder_AA

A shirin na wannan mako, Murtala Zhang ya zanta da malam Abdullahi Tukur Bawa, wani dan Najeriya wanda a yanzu haka yake aiki a wani kamfanin kasar Sin dake arewacin Najeriya, musamman a bangaren aikin noma.

Abdullahi Tukur Bawa: Noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya na da makoma mai haske a Najeriya_fororder_BB

Abdullahi Tukur Bawa, ya yi shekaru 7 yana karatu a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya kuma iya Sinanci da fahimtar halayen al’ummar kasar gami da al’adunsu, abun da ya ba shi kwarin-gwiwar yin aiki da kamfanin Sin. Yanzu, yana aikin bunkasa fasahar noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya a arewacin kasar, wato hybrid rice a turance. A cewarsa, kwararru a fannin aikin gona na kasar Sin, sun kawo sabbin fasahohi da na’urori gami da dabarun aikin gona, abun da zai taimaka sosai wajen warware matsalar karancin abincin dake addabar wasu sassan arewacin Najeriya. (Murtala Zhang)