logo

HAUSA

COVID-19: Rayuwar Amurkawa na cikin tasku

2021-01-04 18:55:03 CRI

COVID-19: Rayuwar Amurkawa na cikin tasku_fororder_0104-1

Masu hikimar magana suna cewa “tsalle guda ake a fada rijiya sai an yi dubu ba a iya fita ba”. Tun bayan bullar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a farkon shekarar da ta gabata an yi ta samun bayanai masu cin karo da juna a tsakanin mahukuntan Amurka, lamarin da ya janyo rudani da cece-ku-ce a tsakanin al’ummar kasar wacce ke ikirarin tutiya da tsarin mulki irin na demokaradiyya. Koda yake, tsarin mulkin demokradiyya ya sahhalewa al’umma ’yancin aiwatar da rayuwarsu yadda suke so. To amma game da yadda shugabannin Amurka suka yi sakaci da rikon sakainar kashi kan batun annobar tun a farkon lamari shi ne musabbabin da ya jefa rayuwar al’ummar kasar cikin mummunan tasirin annobar ta COVID a halin yanzu. Bisa alkaluma na baya bayan nan da cibiyar nazarin kimiyya ta CSSE dake jami’ar Johns Hopkins ta Amurka ta fitar, ya zuwa yammacin ranar Asabar din da ta gabata, adadin Amurkawan da annobar COVID-19 ta hallaka ya zarce 350,000. Yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai miliyan 20 da dubu 400. A cewar alkaluman, jahar New York ta yi hasarar rayukan mutane 38,273, ita ce ke sahun gaba na yawan mutanen da cutar ta kashe a Amurka. Texas tana matsayi na biyu na yawan mutanen da suka mutu 28,338, sai jahar California dake bi mata baya da yawan mutuwa 26,542, Florida ta rasa mutane 21,890, kamar yadda alkaluman CSSE suka nuna. Jahohin da yawan mutuwarsu ya zarce 10,000 sun hada da New Jersey, Illinois, Pennsylvania, Michigan, Massachusetts da jihar Georgia. Amurka ce kasar ta annobar COVID-19 ta fi yiwa barna a duk duniya, ita ce take da adadi mafi yawa na mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar da kuma mutanen dake kamuwa da cutar, inda take da kashi 24 bisa 100 na yawan masu kamuwa da cutar a duk duniya, kana tana da kashi 19 na yawan mutanen da cutar ta kashe a duniya baki daya.

Adadin Amurkawan da COVID-19 ta kashe a cikin kwanaki 19 ya zarce 50,000, bayan cutar ta kashe mutane 300,000 ya zuwa ranar 14 ga watan Disambar shekarar 2020. Sai dai wani abu mai ban tausayi da juyayi shi ne yadda masana suka yi hasashen mummunar hasarar rayukan da za a samu na Amurkawa nan da wasu ’yan kwanaki ko watanni masu zuwa, kamar yadda cibiyar kiwon lafiya da bincike ta jami’ar Washington ta yi hasashen cewa, yawan mutunen da COVID-19 za ta kashe a kasar Amurka zai iya kaiwa 567,195 ya zuwa ranar 1 ga watan Afrilun 2021. Hakika, ya kamata shugabannin Amurka su kara himma domin kada wankin hula ya kai su dare game da wannan masifaffiyar cuta. (Ahmad Fagam)