logo

HAUSA

An samu ci gaba sosai a fannin hada hanyoyin biranen Chengdu da Chongqing dake yammacin Sin

2021-01-04 11:00:43 CRI

A ranar 3 ga watan Janairun bara, kasar Sin ta gabatar da shirin gina wani yanki na raya tattalin arziki, da ya hada biranen Chengdu da Chongqing, dake yammacin kasar. Wannan shiri ya biyo bayan yadda kasar ta tsara wasu shirye-shiryen raya yankin Delta na kogin Yangtse, da yankin mashigin teku da ya kunshi Guangdong, da Hong Kong, da Macau, da yankin Beijing, da Tianjin, da Hebei, duk a gabashin kasar Sin. Zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai a kokarin raya yankin Chengdu-Chongqing, musamman ma a fannonin kirkiro sabbin tsare-tsare, da hada kayayyakin more rayuwa da hanyoyi, da raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da dai sauransu.

Idan aka dauki layin dogo a matsayin misali, a ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2020, aka fara amfani da kan jirgi mai saurin gudu samfurin Fuxing a kan layin dogon da ya hada Chengdu da Chongqing, lamarin da ya rage lokacin da ake bukata wajen tafiya a tsakanin biranen zuwa mintuna 62. Kana kowace rana akwai jiragen kasa masu saurin gudu 175 da suke zirga-zirga a tsakanin biranen 2. Haka zalika, an inganta fasahohin zirga-zirgar jiragen kasa da ya hada Chengdu da Chongqing, da wasu kasashen Turai.

Ban da wannan kuma, a fannin gina tagwayen hanya, an riga an kammala aikin gina hanyoyi 13 daga cikin wasu 25 da aka yi shirin ginawa. Sauran 4 da ake kokarin gina su a halin yanzu.(Bello Wang)

Bello