logo

HAUSA

Shugabar ECA ta bukaci a zurfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu domin cika alkawurran yarjejeniyar AfCFTA

2021-01-03 17:45:18 CRI

A yayin da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta kasashen nahiyar Afrika AfCFTA ta fara aiki a ranar Juma’a, babbar sakatariyar hukumar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ECA, Vera Songwe, ta bukaci a zurfafa hadin gwiwar kut-da-kut a tsakanin gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu karkashin yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta kasashen nahiyar Afrika domin cika alkawurra.

Songwe, ta yaba rawar da yarjejeniyar AfCFTA ta taka wajen bunkasa fannonin zuba jari, da kirkire kirkire domin samar da ci gaba a Afrika.

An dai fara kasuwanci karkashin yarjejejiyar AfCFTA a karon farko, inda kamfanin sufurin jiragen sama na Ethiopian Airlines ya yi jigilar kayayyaki na farko, wanda aka gudanar da bikin a ranar Juma’a a filin jirgin saman kasa da kasa na Bole dake Addis Ababa, babban birnin Habasha.(Ahmad)