logo

HAUSA

Ziyarar Wang Yi a kasashe 5 na Afirka za ta kara inganta zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka

2021-01-03 21:01:11 CRI

Ziyarar Wang Yi a kasashe 5 na Afirka za ta kara inganta zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210103-sharhi-Sanusi Chen-hoto1

Gobe, 4 ga watan Janairun shekarar 2021, Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin zai tashi daga nan Beijing zuwa kasashen Najeriya da Kongo Kinshasa da Botswana da Tanzania da kuma Seychelles, bisa gayyatar da takwarorinsa na wadannan kasashen biyar suka yi masa.

Ziyarar ministan harkokin wajen na Sin zuwa kasashen Afirka, wata muhimmiyar al’ada ce da duk wani ministan harkokin wajen kasar Sin ya saba, an fara kai ziyarar kasashen Afirka a farkon watan kowace shekara ne tun a shekarar 1991, abin da ke nuna cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan raya alakarta da Afirka.

Ziyarar Wang Yi a kasashe 5 na Afirka za ta kara inganta zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210103-sharhi-Sanusi Chen-hoto2

Tun lokacin da annobar COVID-19 ta barke a shekarar 2020, Sin da Afirka sun hada kansu suka kuma yaki wannan annobar tare, abin da ke kara nuna ’yan uwantakar dake tsakanin sassan biyu. Sakamakon haka, ma iya cewa, wannan ziyarar da Wang Yi zai kai wadannan kasashen biyar tana da muhimmanci sosai ga kokarin karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2021.

A yayin taron koli na musamman tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da aka shirya a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2020, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da wani jawabi mai jigo “Tinkarar annobar cikin hadin gwiwa domin shawo kan matsalar tare”, inda ya jaddada cewa, bangaren kasar Sin zai ci gaba da tallafawa kasashen Afirka wajen tinkarar annobar COVID-19. Sabo da haka, a shekarar 2020, a lokacin da kasar Sin take cikin halin fama da annobar, galibin kasashen Afirka sun hanzarta ba mu hannunsu sun aiko mana kayayyakin kandagarkin annobar. Bayan kasar Sin ta samu nasarar shawo kan annobar, ba tare da bata lokaci ba, ta taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar annobar ta hanyoyin samar da dimbin kayayyakin kandagarkin annobar, da tura tawagogin kwararru da jami’an kiwon lafiya zuwa kasashen Afirka, da kaddamar da shirin gina cibiyar yin rigakafi da kuma tinkarar cututuka ta Afirka wato Africa CDC da kuma hanzarta gina wasu asibitoci a wasu kasashen Afirka, ta yadda kasashen Afirka za su iya samun karin karfin tinkarar annobar da sauran cututuka.

Ziyarar Wang Yi a kasashe 5 na Afirka za ta kara inganta zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210103-sharhi-Sanusi Chen-hoto2

A shekarar 2020, koda yake an sha wahalhalu sosai sakamakon barkewar annobar COVID-19 a duk fadin duniya, amma a lokacin da kasashen Sin da Afirka suka kara yin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya, suka kuma kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban. Alal misali, a lokacin da aka shirya bikin baje kolin cinikin harkokin ba da hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin a watan Satumban da ya gabata a nan Beijing, an kuma shirya wani taron musamman a ran 7 ga watan Satumban kan yadda za a kara yin hadin gwiwa a wannan fanni a tsakanin kasashen Sin da Afirka bisa shawarar “Ziri daya da Hanya daya" da dandalin FOCAC.

Bugu da kari, an shirya taron hangen nesa kan sakamakon da aka samu cikin shekaru 20 da suka gabata bayan kafuwar dandalin FOCAC a ran 12 ga watan Oktoba, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall suka aika sakwannin taya murnar cika shekaru 20 da kafuwar FOCAC.

Sannan a karshen watan Oktoban shekarar 2020, karo na biyar ne aka shirya shagalin jin dadin matasan Sin da Afirka a nan kasar Sin, inda matasa 42 daga kasashe daban daban na Afirka sun kai ziyara wasu hukumomin gwamnati da masana’antu da yankunan bunkasa kimiyya da fasaha dake nan Beijing da lardin Jiangxi dake kudancin kasar Sin. A watan Nuwamban, wasu kamfanonin Afirka da yawa sun halarci bikin baje kolin kayayyakin da kasar Sin ke shigowarsu daga ketare karo na uku da aka shirya a birnin Shanghai. Har ma a watan Disamban, an isar da wasu allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Masar. Bangaren kasar Sin ne ya nazarci allurar, kuma aka harhada su a Hadaddiyar daular Larabawa.

Ziyarar Wang Yi a kasashe 5 na Afirka za ta kara inganta zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka_fororder_20210103-sharhi-Sanusi Chen-hoto3

Kasashen Sin da Afirka sun samu sakamako masu yawa ta hanyar yin hadin gwiwa a shekarar 2020. Shekarar 2021, wato shekara ta karshe da ya kamata a kammala dukkan ayyukan da bangaren Sin ya alkawarta ya samar wa kasashen Afirka cikin shekaru 3 da suka gabata bayan taron FOCAC da aka yi a watan Nuwamban shekarar 2018, sannan, za a shirya sabon taron ministocin FOCAC a kasar Senegal a shekarar 2021. Bugu da kari, shekarar 2021 shekara ce ta cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Najeriya, kuma tsakanin kasar Sin da kasar Congo Kinshasa, kuma shekarar cika shekaru 45 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Seychelles. Sakamakon haka, shekarar 2021 tana da muhimmanci sosai ga bangarorin biyu. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a yayin taron koli na musamman tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da aka shirya a ran 17 ga watan Yunin shekarar 2020, cewar za a hanzarta hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka a nan gaba. Sabo da haka, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayar, an ce, a lokacin da Mr. Wang Yi ya kai ziyara kasashen biyar na Afirka, zai tattauna da musayar ra’ayoyinsa da bangarorin kasashen Afirka, ta yadda za a iya tafiyar da harkoki bisa matsaya iri daya da shugabannin kasashen Sin da Afirka suka cimma a yayin tarukan koli na FOCAC da na kasashen Sin da Afirka wajen tinkarar annobar COVID-19, ta yadda za a iya taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar annobar da kuma farfado da tattalin arzikinsu, har ma za a iya hanzarta kafa wata al’umma mai makoma iri daya tsakanin Sin da Afirka. Bugu da kari, zai yi musayar ra’ayoyinsa da bangarorin Afirka wajen shirya sabon taron tattaunawa na FOCAC da za a yi a bana a kasar Senegal. (Sanusi Chen)