logo

HAUSA

Ana kara sa ran dunkulewar nahiyar Afrika yayin aka fara cinikayya karkashin yarjejeniyar AfCFTA

2021-01-02 16:56:02 CRI

An fara cinikayya karkashin yarjejeniyar yankin ciniki mara shinge ta nahiyar Afrika a jiya Juma’a, yayin da ake kara sa ran ganin dunkulewar nahiyar.

Zuwa yanzu, yarjejeniyar wadda aka kaddamar a watan Maris na 2018 a birnin Kigalin Rwanda, ta samu kasashen nahiyar 54 da suka rattaba hannu a kai, lamarin da ya samar da sabuwar fata da murna ta fuskar inganta cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar da kuma saukaka rayawa da bunkasa ayyukan masana’atu. Eritrea ce kasa daya tilo da bata sa hannu kan yarjejeniyar ba.

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ke shugabantar Tarayyar Afrika a wannan karo, ya jaddada cewa, yarjejeniyar yankin cinikayya cikin ‘yanci, za ta samar da gagarumin sauyi ga tattalin arzikin nahiyar.

A cewar hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA), yarjejeniyar na da karfin bunkasa matsayin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar da sama da kaso 52, ya zuwa shekarar 2022.

Da yake taya murnar fara cinikayya karkashin yarjejeniyar, Firaministan kasar Ethiopia, Abiy Ahmed, ya nanata cewa yarjejeniyar cinikayyar za ta karfafa kokarin nahiyar na dunkulewa da samun ci gaba. (Fa’iza Mustapha)