logo

HAUSA

Sharhi: Sabuwar shekara ta 2021 ta bude wani sabon babi na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afirka

2021-01-02 20:14:45 CRI

A jiya Jumma’a ne, an fara aiki da yarjejeniyar ciniki marar shinge a tsakanin kasar Sin da Mauritius, yarjejeniyar da ta kasance ta farko a tsakanin kasar Sin da wata kasar Afirka ta fannin ciniki marar shinge. A wannan rana kuma, an kaddamar da yankin ciniki marar shinge a Afirka (AfCFTA) a hukunce. Ma iya cewa, sabuwar shekara ta 2021 da muka shiga ta bude wani sabon babi na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afirka.

 Sharhi: Sabuwar shekara ta 2021 ta bude wani sabon babi na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20210102200909

Yarjejeniyar ciniki marar shinge a tsakanin Sin da Mauritius ta kasance irinta na farko da aka cimma tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wadda ke da muhimmiyar ma’ana a hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin sassan biyu, wadda kuma ta bayyana niyyar kasar Sin ta goyon bayan ciniki marar shinge da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya. Bayan da ta fara aiki, nau’o’in harajin da kasashen biyu za su cire wa juna za su kai kaso 96.3% da kuma 94.2%. A fannin cinikayyar hidimomi, bangarorin biyu sun kuma yi alkawarin bude sassa sama da 100 ga juna.

Sanin kowa ne kasar Sin tana da babbar kasuwa, kuma kasar ta kasance daya tilo daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya da ta samu karuwar tattalin arziki a bara duk da annobar Covid-19 da ake fuskanta. Sai kuma a bangaren Mauritius, yanzu haka yawan kayayyakin da take shigarwa daga kasar Sin ya wuce wadanda take fitarwa zuwa kasar, don haka, yarjejeniyar za ta taimaka ga daidaita gibin ciniki a tsakaninsu. Aikin samar da sukari wani babban ginshiki ne na tattalin arzikin kasar Mauritius, amma cinikin sukari a tsakanin kasashen biyu ya dade bai samu ci gaba sosai ba. A cewar Devesh Dukhira, shugaban kungiyar masu sana’ar samar da sukari ta kasar Mauritius, tanade-tanaden yarjejeniyar sun bayyana kason sukari da kasar Sin za ta karba daga Mauritius, da kuma yawan harajin da za a saka, matakin da zai sa kaimi matuka ga aikin noman rake da samar da sukari a kasar, wanda kuma zai taimaka sosai ga tabbatar da dauwamammen ci gaban ayyukan samar da sukari a kasar.

Sharhi: Sabuwar shekara ta 2021 ta bude wani sabon babi na hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afirka_fororder_微信图片_20210102200914

Baya ga haka, yankin ciniki maras shinge na nahiyar da aka kaddamar a wannan rana shi ma zai sa kaimin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka, baya ga fatan ganin inganta harkokin ciniki tsakanin kasashen Afirka da kuma bunkasuwar tattalin arziki da ma dunkulewar nahiyar. Kasancewar yankin zai kara janyo jari da kuma kamfanoni daga kasar Sin a sakamakon yadda ya saukaka harkokin ciniki da zuba jari tare kuma da samar da karin damammaki na ciniki. A sa’i daya kuma, kaddamar da yankin ciniki marar shinge a Afirka na bukatar a kara inganta manyan ababen more rayuwa da ba su ci gaba ba a nahiyar, kuma hakan zai samar da damar hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, duba da cewa kasar Sin ta yi fice ta fannin gina ababen more rayuwa.

Abin yabawa ne yadda aka fara aiki da yarjejeniyar ciniki marar shinge a tsakanin Sin da Mauritius da kuma kaddamar da yankin ciniki marar shinge a Afirka a farkon shekarar 2021 da muka shiga, musamman ma a lokacin da ake fuskantar karin kariyar ciniki a fadin duniya, kuma hakan zai taimaka ga farfadowar tattalin arzikin Afirka daga mummunan tasirin annobar Covid-19, tare kuma da kara inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka nan da shekaru masu zuwa. (Lubabatu Lei)