logo

HAUSA

Sin Za Ta Samar da Nau’in Farko Na Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Ga Dukkan Jama’arta

2021-01-01 17:24:36 CRI

Sin Za Ta Samar da Nau’in Farko Na Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Ga Dukkan Jama’arta_fororder_WechatIMG5

Shekarar 2020 shekara ta musamman ga dukkan bil Adam. Cutar COVID-19 ta bazu ba zato ba tsammani a duk fadin duniya, dukkan bil Adam sun fuskanci kalubalen tare. Ban da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar, nazarin alluran rigakafi shi ma ya zama aiki mai muhimmanci sosai a lokacin. A rana ta karshe ta shekarar 2020, kasar Sin ta sanar da wani labari mai jawo hankali sosai, inda ta amince da nau’in farko na rigakafin cutar COVID-19, wanda aka samar a cikin kasar bisa sharadi. Kana a nan gaba, za a samar da shi ga dukkan jama’ar kasar Sin.

A yayin taron manema labarun da majalisar gudanarwar kasar Sin ta gudanar a jiya, an tabbatar da cewa, sakamakon wucin gadi na zagaye na 3 na gwajin rigakafin da aka yiwa mutane, ya shaida cewa tasirin rigakafin ya kai kaso 79.34 bisa dari, wanda ya kai mizanin da WHO, da NMPA suka gindaya kafin fara amfani da kowane irin nau’i na allurar rigakafi.

Tun da aka fara yin bincike da nazarin alluran rigakafin cutar COVID-19, Sin ta kasance a kan gaba a wannan fanni a duniya. Yayin da ake yin nazarin, Sin ta kara maida hankali ga tsaron alluran. A watan Yuni na shekarar 2020, Sin ta fara yin alluran rigakafin cutar COVID-19 ga mutanen da suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar. Ya zuwa karshen watan Nuwanba, yawan mutanen da aka yi alluran a kasar Sin, ya zarce miliyan 1 da dubu 500. A ranar 15 ga watan Disamba, Sin ta kaddamar da aikin yin alluran rigakafin cutar ga mutane na musamman. Bayan kwanaki 15 ke nan, yawan mutanen da aka yi alluran a dukkan fadin kasar Sin, ya zarce miliyan 3. Wannan ya shaida cewa, Sin ta tabbatar da tsaron alluran.

Kana Sin ta samar da alluran ga wasu kasashen duniya da suke bukata, kamar su UAE, Brazil, Argentina da sauransu, wadanda suka yi gwajin alluran, suka kuma amince da tsaronsu tare da shirya yin alluran ga jama’arsu. Wannan ya shaida cewa, allurar rigakafi da kasar Sin ta samar, tana da tsaro, kuma Sin tana son raba da yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya a wannan fanni.

Bisa shirin da mahukuntan kasar Sin suka tsara, a nan gaba, bisa yanayin samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, za a samar da su ga dukkan jama’ar kasar.

Ko da yake an kashe kudade masu tarin yawa wajen yin nazarin alluran, amma rayuka ta fi komai daraja. A don haka, Sin ta fi maida hankali ga rayukan jama’arta. Kana Sin za ta samar da allurar rigakafin ga sauran jama’ar kasashen duniya, wannan ya shaida cewa, al’ummar duniya na zaune ne a waje guda, matsala guda da dukkan bil Adam ke fuskanta tare, kuma Sin tana kokarin sauke nauyi, tare da ba da gudummawarta ga dukkan duniya. (Zainab Zhang)