logo

HAUSA

Kasar Sin tana taimakawa ci gaban duk duniya

2021-01-01 17:25:44 CRI

Kasar Sin tana taimakawa ci gaban duk duniya_fororder_A

A gabannin shiga sabuwar shekara ta 2021, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta kafar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasa gami da yanar gizo ta intanet, inda ya waiwayi dimbin nasarorin da kasarsa ta samu a shekarar da ta gabata, da hango makomar ci gaban kasar a shekara ta 2021, tare kuma da mika sakon fatan alheri. Ana iya ganin cewa, a shekarar da ta gabata, babban karfin da kasar Sin take da shi, ba karfafawa al’ummarta gwiwar haye wahalhalu kawai ya yi ba, har ma ya sanya sabon kuzari ga gamayyar kasa da kasa, domin sa kaimi ga ci gaban duniya, duk da mawuyacin halin da take ciki.

A shekara ta 2020, annobar COVID-19 ta ci gaba da bazuwa a duniya, abun da ya janyo tawayar tattalin arzikin duniya mafi muni, da ba a taba ganin irinsa ba, tun barkewar yakin duniya na biyu, amma akasin haka, kasar Sin ta samu dimbin nasarori wadanda suka jawo hankalin duniya sosai da sosai. Har wa yau, kasar tana himmatuwa wajen gudanar da hadin-gwiwa tare da sauran kasashe domin dakile yaduwar cutar, da bayyanawa duk duniya ainihin ma’anar “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya”.

Kasar Sin tana taimakawa ci gaban duk duniya_fororder_B

A yayin da duniya ke kara dunkulewa waje daya, tattalin arzikin kasar Sin yana karuwa, al’amarin da ya samar da babban zarafi ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta ci gaba da zama jigon samun ci gaban tattalin arzikin duniya, da kyautata rayuwar al’umma ta hanyar kimiyya, da cimma burin kawar da matsanancin talauci a kasar da kuma taimakawa kokarin rage talauci a duk duinya. Irin wadannan nasarorin da kasar Sin ta samu, ba nata ne kawai ba, na duinya ne baki daya.

Idan muka waiwayi abubuwan da suka wakana a baya, zai taimaka mana wajen kara samun ci gaba. Sabuwar shekara ta 2021, shekaru 100 ke nan da kafa jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shekarar farko da kasar Sin ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, gami da bude sabon babi na raya kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkanin fannoni. Duniya tana da kyakkyawan fata kan makomar kasar Sin.(Murtala Zhang)