logo

HAUSA

Yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai za ta amfani kowane bangare

2020-12-31 20:45:57 CRI

Yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai za ta amfani kowane bangare_fororder_A

Da maraicen jiya Laraba, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi shawarwari ta kafar bidiyo tare da wasu takwarorin aikinsa na kasashen Turai, ciki har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban majalisar nahiyar Turai Charles Michel, da kuma shugabar gudanarwar tarayyar Turai Ursula von der Leyen, inda suka sanar da kammala shawarwarin da suka yi kan yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai kamar yadda aka tsara.

Bayan da aka shafe tsawon shekaru 7 ana gudanar da shawarwari har zagaye 35, yanzu ana iya cewa, an cimma tudun dafawa game da yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai. Duk da cewa akwai wasu matakai da suka rage, ciki har da sanya hannu gami da nazartar yarjejeniyar, yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma-baya sosai sakamakon annobar COVID-19, kammala shawarwarin kan yarjejeniyar, wani albishiri ne ga kowane bangare.

Yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai za ta amfani kowane bangare_fororder_B

A bangaren kasar Sin, baya ga yadda yarjejeniyar za ta taimaka wajen zubawa juna jari, za kuma ta sa kaimi ga kasar Sin ta kara bude kofarta ga kasashen waje, da samar da ci gaba mai inganci.

A bangaren nahiyar Turai ma, yarjejeniyar ta zo a lokacin da ake da bukata. Sakamakon yaduwar annobar COVID-19, duk da cewa daga watan Yuli zuwa Satumbar shekara ta 2020, tattalin arziki na tarayyar Turai da na yankuna masu amfani da kudin EURO duk ya samu farfadowa, amma ya ragu idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekara ta 2019. Har yanzu ba’a taka birki ga yaduwar annobar a Turai ba, kuma akwai bukatar karin taimako da goyon-baya wajen farfado da tattalin arzikin kasashen nahiyar. A sabili da haka, fadada hadin-gwiwa tare da kasar Sin, tana daya daga cikin aminan kasuwanci mafi muhimmanci a duniya, kyakkyawan zabi ne ga tarayyar Turai wato EU.

A dayan hannu kuma, yarjejeniyar ta kasance wadda duniya take sa ran gani. Sanin kowa ne cewa, shekara ta 2020, shekara ce mai wahalar gaske, duba da yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa, da yadda ra’ayin bada kariya ke ci gaba da karuwa, kana tattalin arzikin duniya ke fuskantar babban kalubale. A wannan muhimmin lokaci, ya zama dole Sin da Turai su yi aiki kafada da kafada, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, yarjejeniyar za ta amfanawa farfadowar tattalin arzikin duniya, da saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari a duniya, ta yadda Sin da Turai za su bada muhimmiyar gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa.(Murtala Zhang)