logo

HAUSA

2020: Sin ta kasance abin koyi wajen yaki da talaucin bil Adama

2020-12-31 10:47:56 CRI

A shekarar 2020 dake daf da karewa, kasar Sin ta cimma burinta na fitar da daukacin al’ummar kasar daga kangin talauci, inda ta kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya.

2020: Sin ta kasance abin koyi wajen yaki da talaucin bil Adama_fororder_1

Gasasshiyar agwagwa ta birnin Beijing, abincin gargajiya ne na kasar Sin, wanda ya fi shahara a fadin duniya, duk wanda ya zo nan Beijing, domin aiki ko yawon shakatawa ko haduwa da dangogi, tabbas zai dandana agwagwar Beijing.

To sai dai fa mai yiwuwa ne kana dandana agwawar da aka gasa a birnin Beijing ne, amma kuma an yi kiwon ta, da kuma jigilar ta ne daga gundumar Lop ta yankin Hetian na jihar Xinjiang, wadda ke da nisan kilomita sama da 4000 daga birnin. Abun farin ciki shi ne, gundumar Lop ta cimma burin fitar daga kangin talauci ta hanyar kiwon Agwagwi, tare kuma da sayar da su zuwa nan Beijing.

Gundumar Lop tana kan hamadar Taklimakan ne, inda fadin wurin ciyayinta bai kai kaso 6 bisa dari bisa daukacin fadin gundumar ba. A don haka gundumar ta taba fama da talauci saboda karancin gonaki.

A shekarar 2017, birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ya kulla huldar taimakawa gundumar Lop, ta hanyar gina sansanin kiwon agwagwi a wurin.

2020: Sin ta kasance abin koyi wajen yaki da talaucin bil Adama_fororder_2

Mai kiwon agwagwi a kamfanin hadin gwiwar sana’a na manoman kiwon tsuntsayen gida na gundumar Lop Abulaiti Rejiepu, yana da shekarun haihuwa 25 a baya. Ya taba shuka hatsi a gonaki, amma ya samu kudin shiga kadan ne, haka kuma ya taba fama da kangin talauci, daga baya ya fara aiki a kamfanin hadin gwiwar tun daga watan Satumban shekarar bara ta 2019, cikin sauri kuma ya kware a bangaren kiwon agwagwi, bayan da masana suka ba shi horo. Yanzu dai adadin kudin shigarsa a ko wane wata ya kai fiye da yuan 3000. Ya gaya mana cewa, tun farkon da ya fara aiki a nan, bai saba ba saboda bai taba ganin agwagi da yawa irin haka ba, amma yanzu yana son agwagwi matuka. An lura cewa, a gundumar Lop, gaba daya iyalai wadanda suka samu wadata ta hanyar gudanar da ayyukan dake da nasaba da kiwon agwagwi sun kai wajen 5000.

Hakika tun daga shekarar 2012, wato tun bayan da shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da umurnin fitar da al’ummun kasar daga kangin talauci, nan da nan gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin yankunan gabashin kasar da na yammacin kasar, domin cimma burin fitar da daukacin al’ummun kasar daga kangin talauci.

Alal misali, yankuna masu ci gaba dake gabashin kasar, sun tura kwarraru, da kuma samar da taimakon kudi ga yankunan da ba su da iyaka da teku dake yammacin kasar, ta yadda za su cimma buri na samun wadata tare. huldar hadin gwiwar dake tsakanin birnin Beijing da yankin Hetian na jihar Xinjing, daya ne daga cikinsu.

2020: Sin ta kasance abin koyi wajen yaki da talaucin bil Adama_fororder_4

Kawo yanzu wato bayan kokarin da Sinawa suka yi a cikin shekaru 8 da suka gabata, kasar Sin ta riga ta cimma burinta na fitar da daukacin al’ummunta daga kangin talauci, al’ummunta da yawansu ya kai miliyan 100 sun fita daga fatara cikin nasara.

Mamadou Fall, farfesan jami’ar Cheikh Anta Diop ta kasar Senegal ya bayyana cewa, salon yaki da talauci na kasar Sin, ya kasance abin koyi ga kasashen Afirka, har ma ya kasance abin koyi ga daukacin kasashen duniya. Yana mai cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin tana jagorancin al’ummun kasarta, ta hanyoyi daban daban, kamar su aiwatar manufar yin gyare gyare a gida da kuma bude kofa ga ketare, domin ciyar da kasarsu gaba yadda ya kamata, don haka ya dace a koyi karfin ba da jagora na gwamnatin kasar Sin.

Guo Shengxiang, masanin harkokin tattalin arzikin kasar Australia ya yi nuni da cewa, manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga ketare ta kasar Sin, ta sa kaimi ga aikin yaki da talauci a kasar. A sa’i daya kuma, sakamakon yaki da talauci na kasar, shi ma ya taimakawa ci gaban tattalin arziki a kasar, har ya ba da gudummowa ga karuwar tattalin arzikin duniya.

Shi ma shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta kasar Brazil Ronnie Lins, ya furta cewa, kasar Sin ta dauki matakan hana al’ummun kasarta su sake shiga yanayin talauci, ta hanyar kyautata tsarin tattalin arziki, da kyautata tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar al’umma, da kuma kara karfafa aikin ba da ilmi a kasar, duk wadannan sun samar da tunani, da salo wajen yaki da talauci ga kasashen duniya da dama.

Daraktar sashen nazarin harkokin kasar Sin na cibiyar nazarin tsare-tsaren kasa da kasa ta kasar Indonesia Veronika S. Saraswati, ita ma na ganin cewa, babban sakamakon da kasar Sin ta samu a bangaren yaki da talauci, ya ba da misali ga sauran kasashe masu tasowa, yayin da suke kokarin cimma burin samun ci gaba mai dorewa. (Jamila)