logo

HAUSA

Dabara ta Rage ga mai Shiga Rijiya

2020-12-30 18:51:51 CRI

Dabara ta Rage ga mai Shiga Rijiya_fororder_微信图片_20201230174259

Sannu-Sannu aka ce ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a zo ba, yanzu dai ta tabbata cewa, yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka (AfCFTA) za ta fara a hukumance a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021, bayan da kasashen nahiyar kusan 54 suka amince da ita.

Fara aiki da wannan yarjejeniya, tamkar cika buri ne na jagororin da suka kafa tsohuwar kungiyar hadin kan Afirka(OAU) wato kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yanzu, na neman raya makomar nahiyar. Wannan mataki zai baiwa kasashen nahiyar damar tallatawa da cin gajiyar albarkatun da Allah ya hore musu, ta hanyar cinikayya ba tare da wani shamaki ba, matakin da ya kai ga tsara ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.

Wannan ne ma ya sa babban jami'in cibiyar kula da manufofin cinikayyar Afirka (ATPC) na hukumar kula da tattalin arzikin Afirka na MDD wato UNECA David Luke, ya bayyana cewa, ya kamata a sakarwa yarjejeniyar mara ta yi aiki yadda ya kamata, kasancewarta hanya mafi dacewa ga nahiyar ta samun dauwamammen ci gaba.

Sanin kowa ne cewa, al’umma tana samun ci gaba ne, lokacin da jama’arta suka fadada karfinsu na samar da kaya, da ingancin aiki da takara, ta hanyar cinikayya, kuma bai Afirka ta zama saniyar ware ba.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya, cibiyar masana kan dunkulewar kasar Sin da kasashen duniya, tare da hadin gwiwar AU, suka kira wani taron tattaunawa da jakadu, da manyan jami’ai da wakilan ofisoshin jakadanci sama da 50 dake Sin, da ’yan kasuwar Sin dake gudanar da harkokin kasuwanci a Afirka, game da manufar kasar Sin ta bude kofa da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 da ma yarjejeniyar ta AfCTA. Ta yadda bangarori biyu, wato Sin da Afirka za su amfana da juna.

A matsayinta na babbar kasuwa wato kasar Sin, yayin da Afirka ke da tarin albarkatu da matasa masu basira, sassan biyu za su amfana, kasancewarsu muhimman kawaye dake da kyakkyawar alaka ta mutunta juna. Yanzu dai ya rage ga kasashen nahiyar, kan yadda za su ji gajiyar yarjejeniyar kasuwa ta bai daya ta kasashe 55, wadda za a gudanar da cinikayyar hajoji, da hidima, da daidaita duk wata matsalar cinikayyar da ta kunno kai, da batun zuba jari, da ’yancin mallakar fasaha, da yin takara da cinikayya ta yanar gizo da sauransu.

Idan har aka aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, wadda jami’an nahiyar suka ce, babu wani shiri na biyu game da wannan yarjejeniya, ana fatan za ta fitar da mutane miliyan 30 daga kangin talauci tare da inganta rayuwar mutane miliyan 68 dake rayuwa a kasa da dala biyar a rana, bisa ma’aunin bankin duniya. A don haka, zabi yanzu ya rage ga kasashen nahiyar, ko dai su ci gajiyar yarjejeniyar har ma ta kai nahiyar ga samun ci gaba mai dorewa da aka dade ana hankoron samu, ko su barar da wannan dama. (Ibrahim Yaya)