logo

HAUSA

Kasar Sin tana taimakawa duniya wajen samun ci gaba mai dorewa

2020-12-30 19:39:51 CRI

Kasar Sin tana taimakawa duniya wajen samun ci gaba mai dorewa_fororder_A

Idan har za’a zabi labarin da ya shafi batun sauyin yanayi, a matsayin wanda ya fi jawo hankali a shekara ta 2020, abun da ya faru a ranar 22 ga watan Satumba, ko shakka babu zai kasance a ciki, inda a ranar, a yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta yi alkawarin cewa, kafin shekara ta 2030, ba za ta kara fitar da iskar Carbon Dioxide ba, wato idan adadin ya kai matsayin koli zai ci gaba da raguwa. Sa’annan kafin shekara ta 2060, game da yawan iskar Carbon Dioxide da ta fitar, shi ma za ta dauki duk wani mataki na rage illolinta, ciki har da dasa itatuwa da yin tsimin makamashi da sauransu. A matsayin ta na kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, a karon farko, kasar Sin ta tsara wani tartibin lokaci na cimma burin rage illolin iskar Carbon Dioxide mai gurbata muhalli da take fitarwa, wannan muhimmin mataki ne da ta dauka a fannin samar da dauwamammen ci gaba a duniya.

Kasar Sin tana taimakawa duniya wajen samun ci gaba mai dorewa_fororder_C

Muna iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu wajen kyautata muhallin halittu a kasar Sin a shekaru biyar da suka gabata. Kasar Sin tana himmatuwa wajen kyautata muhalli a duk fadin duniya, kuma a halin yanzu, tana hada kai da kasashe da yankuna sama da 100 a fannonin da suka shafi kasuwancin makamashi, da zuba jari, da na’urori da fasahohi da sauransu.

Bisa shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 da kasar Sin ta tsara, nan da shekaru biyar dake tafe, kasar za ta samu karin ci gaba a fannin sauya salon rayuwa mai salon kiyaye muhallin halittu, kana, za’a dada rage yawan abubuwa masu gurbata muhallin da take fitarwa. Muna iya cewa, a karkashin jagorancin sabon ra’ayin samar da ci gaba, kasar Sin mai cika alkawarin da ta dauka, za ta ci gaba da raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma ba tare da gurbata muhalli ba, da kokarin neman cimma burinta a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayi.(Murtala Zhang)