logo

HAUSA

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci

2020-12-30 21:50:33 CRI

Masu sauraro, kuna dai sauraron wata waka mai taken “gari na mata kyawawa”, wakar da shahararren mai tsara wakoki na kasar Sin Mr.Li Jinhui ya tsara a shekarar 1928, wadda ta yi farin jini sosai a shekarun 1930 a nan kasar Sin har ma a wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya, wadda har ta kara fito da sunan wani wuri mai suna Taojiang. A wakar an yi wa wurin kirarin “gari na mata kyawawa”, a sakamakon yadda ake yawan samun kyawawan mata a wurin.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232051

Gundumar Taojiang dake karkashin birnin Yiyang na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, wuri ne mai matukar ni’ima, wadda baya ga kyawawan mata, ta kuma shahara a matsayin “garin gora”, a sakamakon yawan gora da Allah ya hore su, wadanda fadinsu ya kai kimanin kadada sama da dubu 75, adadin da ya sa ta zama ta uku a kasar Sin ta fannin fadin gonaki na gora. A gundumar, kusan kowa na sana’ar da ta shafi gora, ciki har da samar da tabarma da nau’o’in kayayyakin gida da gora. Baya ga haka, tsiron gora ma ya kasance abinci mai dadi ga mazauna wurin.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230233153

Yiyanglun wani kauye ne da ke karkarar gundumar Taojiang, wanda in ka shiga, babu abin da za ka ji, sai haushin kare da carar zaji, ga kuma wani rafi da ke malala da kuma duwatsu makare da bishiyoyin gora da suka kewaye kauyen. Sai dai mazan dake kauyen da yawa da ko suka kai shekaru 30 zuwa 40 ba su yi aure ba sabo da talauci. Malam Wang Jianjun, jagoran kauyen ya ce,“A hakika, rashin samun ci gaban tattalin arziki ya sa sun kasa yin aure. Wasunsu sun auri matan da aka gabatar musu daga wasu larduna, amma da yawa daga matan sun tafi bayan sun haihu, ko ba su haihu ba sai su tafi, sabo da kasa jure irin talaucin da ake fuskanta a kauyen. A kalla magidanta 20 dake fama da talauci ne suka samu kansu cikin irin matsala.”

Kauyen Yiyanglun na da mazauna 2852, kuma daga cikinsu, akwai mutane 414 da a baya suka kasance cikin kangin talauci. Malam Wang Jianjun ya ce, kasancewar kauyen a cikin duwatsu, zirga-zirga na da wuya a sakamakon rashin ingantattun hanyoyi, don haka, duk da albarkatun gora da suke da su, amma da wuya su sayar da gora ga sassan da ke da wannan bukata.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232228

Malam Liu Manyu na daya daga cikin mazauna kauyen, wanda a shekarar 2014 ne aka yi rajistarsa a matsayin mai fama da talauci. Ya ce, yana da gonakin gora da ya kai kusan kadada 2.5, amma a baya ya bar sun lalace. Ya ce,“Babu hanyoyi, da wuya mu kai gorarmu wasu sassa, ko da mun sayar, kudin da muke samu, bai taka kara ya karya ba , sannan ba zai baya muka biya kudin kwadagon da suka sare su da kuma kudin jigilarsu ba.”

A shekarar 2012, ya gamu da ciwon kugu, lamarin da ya sa malamin ya yi shekara guda yana hutuwa a gida, don haka ba ya da kudin shiga, wannan ya sa uwargidansa ta kashe aure su. A lokacin, yana kuma ciyar da tagwayensu biyu, gaskiya ya sha wahala sosai.

Amma me ya sa ake fuskantar irin wannan kunci a kauyen? A game da wannan tambayar, malam Wang Jianjun, jagoran kauyen yana ganin cewa, dalilin shi ne rashin kamfanoni da masana’antu da suke son zuba jari su gudanar da harkokinsu a kauyen a sakamakon rashin ci gaban ababen more rayuwa da suka hada da ingantattun hanyoyi da kuma wutar lantarki. Yana mai  cewa,“Karancin kamfanonin da suke zuwa don zuba jari a kauyenmu ne ya sa haka. Sabo da me? Wasu ba su da wata fasahar da suka kware, don haka, ko sun tafi cin rani ma ba za a dauke su aiki ba. Wasu suna noman masara da gyada da doya a gida, amma dan kudi kadan suke iya samu daga aikin.”

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230233715

Amma yanayin ya sauya a shekarar 2017, bayan da hukumar gundumar Taojiang ta ba da shawarar bunkasa aikin noman tsiron gora a kauyen, duba da cewa, kauyen Yiyanglun yana da albarkatun bishiyoyin gora da fadinsu ya kai sama da eka dubu 20, ga shi kuma tsiron gora yana samun karbuwa sosai a kasuwa a matsayin nau’in abinci mai dadi.

A daidai wancan lokaci kuma, malam He Zhen mazaunin wannan kauye da a baya ya fita cin rani kuma ya samu akheri ya koma gida, sai malam Wang Jianjun, jagoran kauyen ya je gidansa ya shawarce shi da ya kafa masana’antar sarrafa tsiron gora a kauyen, don jagorantar mazauna kauyen wajen bunkasa aikin noman tsiron gora. Bayan ya tattauna da iyalansa, malam He Zhen ya yarda, don ya gano damammaki a harkar. A karshen shekarar, aka fara kafa ma’aikatar kamfanin samar da tsiron gora a kauyen, kuma a bara kamfanin ya fara aiki a hukunce. Kamfanin yana hadin gwiwa da manoman kauye, wato manoman kauyen suna kulawa da aikin noman tsiron gora, yayin da kamfanin ke samar musu fasahohin noman da kuma takin da za a saka a kyauta, sa’an nan, bayan da manoman suka yi girbi, kamfanin zai sayi tsiron gora daga wajensu kan farashin da ya dan haura na kasuwa, kuma ya sarrafa tsiron zuwa nau’o’in kayayyaki ya sayar.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232245

Malam Liu Manyu shi ma ya shiga kamfanin, ya ce, yanzu yana noma gonakin gora da fadinsu ya kai kadada kimanin 2.5, kuma kamfanin tare da hukumar kula da dazuzzukan gundumar suna samar masa gundumawar fasahohin kulawa da gora da kuma taki. Ya ce,“A bara, ya girbe tsiron gora da suka kai sama da kilogiram 4000, wadanda suka janyo mana karin kudin shigar da ya kai yuan kimanin dubu 10. A bana, sakamakon fasahohin zamani da kuma takin da aka saka, yawan tsiron goran da na samu ya ninka na bara.”

Da ya juya ga ‘ya’yansa, Mr.Liu Manyu ya yi farin ciki da cewa, tagwayensa biyu duka sun ci jarrabawar shiga jami’a, kuma yanzu haka suna karatun digiri na farko a birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan. Kudin shigarsa ya isa ya biya musu kudin makaranta, ga shi kuma suna samun gudummawar kudi da ya kai yuan 3000 a kowace shekara da gwamnati ta samar wa ‘ya’yan masu fama da talauci, yanzu wahalarsa ta kare.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232139

Sinawa na da dadaddiyar al’adar yin amfani da gora, kusan a dukkanin fannoni na rayuwarsu, don haka, kasar tana kan gaba wajen bunkasa harkokin da suka shafi gora. A matsayinsa na “gari na gora”, a gundumar Taojiang, kusan kowa na sana’ar da ta shafi gora, ciki har da samar da tabarma da nau’o’in kayayyakin gida da gora, lalle fasahohin sarrafa gora sun yi ta kara yalwata da inganta a gundumar daga zuriya zuwa zuriya.

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232000

Malam Wang Shenglian shi ma ya gaji fasahar ce daga mahaifinsa, kuma kawo yanzu ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin samar da nau’o’in kayayyaki da gora. Kwana nan kuma, yana kawata gidansa da gora.

A gidansa, kujeru da teburi da zane-zane dukkansu malamin ne da kansa ya sarrafa su da gora, wadanda suke da kyau kwarai. A shekarun 1990, malamin ya sayar da kayayyakinsa zuwa Japan da ma sauran wasu kasashen duniya. A shekarar 2017, ya yayata fasahar zuwa nahiyar Afirka.  A lokacin, ya je kasar Habasha, inda ya shafe sama da kwanaki 30 yana koyar da wasu ‘yan kasar sama da 40 fasahohin sarrafa kayayyaki da gora. Yana mai cewa,“Na koya musu fasahohin sarrafa kujeru da tebura da gado da gora, mun sarrafa nau’o’in kayayyaki da yawa.”

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232402

Malam Wang Shenglian na daya daga cikin malamai uku da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa Habasha tare da hadin gwiwar kungiyar kula da itatuwan gora da rattan ta kasa da kasa, don samar da kwas din koyar da ‘yan kasar fasahohin sarrafa kayayyaki da gora. A hakika, a shekarun 1970, gwamnatin kasar Sin ta tura wasu malamai biyu da suka kware wajen sarrafa gora daga birnin Yiyang zuwa kasar Habasha, wadanda suka shafe tsawon shekaru biyu suna koyar da ‘yan Habasha fasahar sarrafa nau’o’in kayayyaki da gora. Bayan da malaman suka bar kasar, wadanda suka bi su koyon fasahar sun kafa ma’aikatar sarrafa kayayyaki da gora, baya ga zama malamai, suna kuma ci gaba da koyar da fasahar ga sauran ‘yan kasar Habasha.

A shekarar 2002, Habasha ta shiga kungiyar kula da itatuwan gora da ratten ta kasa da kasa, kungiyar da ke dukufa a kan habaka yin amfani da albarkatun gora da ratten, don taimakawa wajen tabbatar da cimma dauwamammen ci gaba a duniya. Dr.Fu Jinhe, darektan ofishin kungiyar da ke kasar Habasha ya ce, Habasha kasa ce da Allah ya albarkace ta da itatuwan gora masu yawa da fadinsu ya kai kadada miliyan 1.47, sai dai ba a bunkasa yin amfani da albarkatun sosai ba a kasar. Daga shekarar 2005 zuwa ta 2006, kungiyar ta hada gwiwa da gwamnatin kasar Sin, inda ta rika gayyatar malaman kasar zuwa Habasha, don samar da kwasa-kwasai na koyar da fasahar sarrafa kayayyaki da gora. Daga nan kuma, kungiyar ta yi ta gayyatar malaman kasar zuwa Habasha a kai a kai. Malam Fu Jinhe ya ce,“A birnin Adis Ababa, akwai wani titi mai dimbin ma’aikatun sarrafa kayayyakin gora a gefunanta, wadanda suke samar da kujeru da tabura da sauran kayayyaki da suka sarrafa da gora. In an dubi fasalin kayayyakin, za a ga irin na kasar Sin ne, kuma hakan ya samo asali ne daga malaman da aka gayyata zuwa nan daga birnin Yiyang shekaru kimanin 50 da suka wuce, tare kuma da kwasa-kwasan da kungiyarmu ta fara samarwa a shekarar 2005. A titin, a kalla akwai ma’aikatu 400 zuwa 500. Ban da Adis Ababa, a sauran biranen kasar ma, akwai irin wannan titi na sayar da kayayyakin gora. A hakika fasahohin kasar Sin sun taimaka wa wadannan ma’aikata wajen samun abin da za su iya dogaro a kai.”

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232351

Malam Wang Shenglian ya ce, dalibansa ‘yan Habasha sun nuna sha’awa sosai kan fasahohin samar da kayayyaki da gora, kuma sun koya har sun iya bayan da kwas ya kare, wasunsu har sun kware. Abin da ya fi faranta wa ani rai shi ne, wani dalibinsa ya samu odar kayan gora bayan da ya gama koyon fasahar. Malam Wang Shenglian ya tuna da cewa,“A lokacin, ta tafinta ne wani dalibi ya ce mini ya samu odar kaya daga wata makaranta, wato samar da tabura da aka sarrafa da gora ga daliban makarantar.”

Sai dai a ganin malam Fu Jinhe, a cikin ‘yan shekarun baya, ba a samu ci gaban ayyukan sarrafa kayayyaki da gora ba a kasar Habasha idan an kwatanta ta da kasar Sin. Amma mene ne dalili? Kasancewar Habasha tana da albarkatun gora da kuma bukatun kayayyakin. Ya ce, dalili shi ne rashin jarin da aka zuba na kafa masana’antun sarrafa kayayyakin. Yana mai cewa,“Don haka, mun rika ba kamfanonin kasar Sin da suke da fasaha kwarin gwiwar zuba jari a Habasha, don taimaka wa kasar, a sa’i daya kuma,  don su kansu su kara samun ci gaba.”

Yadda albarkatun icen gora suka taimaka ga fitar da al'umma daga kangin talauci_fororder_微信图片_20201230232308

Kasancewar gora yana fita da sauri, wanda kuma ke iya taimakawa wajen kiyaye muhalli, a zamanin da muke ciki, an kara bunkasa fannonin da ake amfani da shi, inda ake iya sarrafa nau’o’in kayayyaki sama da dubu 10 da gorar, ciki har da kayayyakin gine-gine da magunguna da riguna da dai sauransu, tare da samar da guraben aikin yi da kuma karin kudin shiga ga al’ummar da ke fama da talauci.

Malam Fu Jinhe ya ce, Afirka nahiya ce da Allah ya albarkace ta da itatuwan gora, ban da Habasha, an kuma gano albarkatun a wasu kasashe 11 da suka hada da Nijeriya da Kamaru da Ghana da dai sauransu. A Nijeriya, fadin itatuwan gora da aka gano sun kai kadada miliyan 1.59. Don haka, akwai kyakkyawar damar bunkasa tattalin arziki bisa gudanar da ayyukan samar da kayayyaki da gora.

A wannan shekara, ragowar magidanta uku da ke kauyen Yiyanglun sun fita daga talauci. Sai kuma a kasar Habasha, ayyukan samar da kayayyaki da albarkatun gora na bunkasa cikin sauri, wadanda suke taimakawa ga fitar da karin al’umma daga kangin talauci. A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2018 a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya sanar da kafa cibiyar gora ta Sin da Afirka, don taimakawa kasashen Afirka bunkasa yin amfani da albarkatun gora, cibiyar da za ta fara aiki a hukunce a shekara mai zuwa, wadda kuma zai ta taimaka ga yayata fasahohin yin amfani da albarkatun gora a tsakanin Sin da kasashen Afirka, a kokarin sa kaimin yin amfani da albarkatun gora da kuma tabbatar da dauwamammen ci gaban ba tare da gurbata muhalli ba a Afirka.