logo

HAUSA

Kasar Sin: Bunkasuwar Masana’antun Sararin Samaniya A Shekarar 2020

2020-12-29 11:14:20 CRI

Shekarar 2020 wata shekara ce ta musamman ga al’ummun kasa da kasa. Kuma a wannan shekara, kasar Sin ta sami gaggarumin ci gaba a fannin raya masana’antun sararin samaniya, kuma dukkanin sakamakon da ta samu sun janyo hankulan al’ummomin kasa da kasa, wadanda za su shiga tarihin kasa da kasa.

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ta debo samfura da dawowa duniyarmu lami lafiya a karo na farko. Kana, a halin yanzu, na’urar binciken duniyar Mars ta Tianwen-1, ta yi nisan kilomita sama da miliyan dari daya da duniyarmu, kuma tana ci gaba a kan hanyarta zuwan duniyar Mars.

Bugu da kari, ana amfani da tsarin taurarin dan Adam mai aikin hidimar taswira na BeiDou-3 da aka bude a karshen watan Yuli a kasashe 120. Dukkansu sun nuna manyan sakamakon da kasar Sin ta samu a shekarar 2020, a fannin raya masana’antun sararin samaniya, kuma ta cimma alkawarinta na amfani da albarkatun sararin samaniya cikin hadin gwiwa da zaman lafiya.

Kasar Sin: Bunkasuwar Masana’antun Sararin Samaniya A Shekarar 2020_fororder_201229-rahoto-maryam-hoto1

Tsarin taurarin dan Adam mai aikin hidimar taswira na BeiDou-3 da aka kammala a ranar 23 ga watan Yuni na bana, shi ne tsarin taurarin dan Adam mai aikin hidimar taswira na hudu da aka kafa a duniya, bayan tsarin GPS na kasar Amurka, da tsarin Glonass na kasar Rasha, da kuma tsarin Galileo na kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU. Kuma, kasar Sin ta fara ba da hidimar taswira ga mutanen dake yankin Asiya da Pasifik, bayan ta kafa tsarin taurarin dan Adam mai aikin hidimar taswira ta BeiDou-2 a shekarar 2012.

Babban darektan tsara aikin taurarin dan Adam mai ba da hidimar taswira na BeiDou-3 Xie Jun ya bayyana a birnin Beijing cewa, bayan kaddamar da tsarin BeiDou-3, a halin yanzu, ana amfani da wannan tsari a fannoni daban daban a kasashe 120 na duniya. Kuma, cikin ‘yan kwanakin nan, kasar Sin ta kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin amfani da tsaron BeiDou-3 da kasar Argentina.

A yayin da yake tsokaci kan bunkasuwar aikin hidimar taswira, Xie Jun ya ce, kasar Sin za ta mai da hankali kan gina wani sabon tsarin taurarin dan Adam mai aikin hidimar taswira, domin biyan bukatun al’ummomin kasa da kasa na jin dadin zamansu.

Kasar Sin: Bunkasuwar Masana’antun Sararin Samaniya A Shekarar 2020_fororder_2

A safiyar ranar 17 ga watan Disamba, na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, ta dawo gida da wasu samfurori daga duniyar wata, kuma wannan shi ne karo na farko da aka dauko samfurori daga duniyar wata cikin shekaru 44 da suka gabata.

Kafin shekaru 50, samfurorin da kasar Amurka ta dawo da su daga duniyar wata, sun baiwa al’ummomin damar nazarin canjawar duniyar wata. Kana, a wannan karo, na’urar Chang’e-5 ta sauka a wani bangare na duniyar wata da ba a taba zuwa ba, inda ta debo samfurorin duwatsu bayan barkewar dutse mai aman wuta a duniyar wata kafin shekaru biliyan 2 da suka gabata. Kuma, samfurorin da aka samu, za su kara fahimtar da al’umma game da tarihin duniyar wata, ta yadda za a kara nazari kan bunkasuwar tsarin tafiyar duniyoyi masu kewaya rana.

Kasar Sin: Bunkasuwar Masana’antun Sararin Samaniya A Shekarar 2020_fororder_201229-rahoto-maryam-hoto2

Bugu da kari, a lokacin dawowar na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, wata na’urar binciken duniyar Mars ta Tianwen-1 tana kan hanyarta zuwa duniyar Mars. Bisa shirin da aka tsara, zuwa karshen shekarar bana, za ta kai nisan kilomita sama da miliyan dari daya da duniyarmu, sa’an nan, za ta shiga hanyar kewaya duniyar Mars a watan Fabrairu na shekarar 2021 mai zuwa.

Ban da kasar Sin, a bana, tarayyar kasashen Larabawa ta harba na’urar binciken duniyar Mars ta Al-Amal, kuma kasar Amurka ta harba motar binciken duniyar Mars ta Perseverance. Sabo da masu aikin kimiyya da fasaha suna son gano asalin rayuwa ta hanyar nazarin duniyar Mars. Ta yadda, dukkanin bil Adama za su kara saninsu game da rayuwa ta kansu, da duniyoyin da muke ciki, sa’an nan, za a gano hanyar da ta dace da bunkasuwar dukkanin bil Adama. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)