logo

HAUSA

Kawar da talauci bisa shirin da aka tsara a Sin ya haskaka yanayin da duniya take ciki

2020-12-29 16:16:00 CRI

Kawar da talauci bisa shirin da aka tsara a Sin ya haskaka yanayin da duniya take ciki_fororder_1229-2

A shekarar 2020, Sin ta tinkari abkuwar cutar COVID-19, kana ta warware matsalar fama da talauci da wasu jama’ar ta ke fuskanta, wadanda kudin shigar su ba sa iya biyan bukatun zaman rayuwarsu a yankuna daban daban bisa shirin da aka tsara, da kuma cimma burin yaki da talauci bisa ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta MDD ta shekarar 2030 kafin shekaru 10, kana Sin ta samar da gudummawar yaki da talauci fiye da kashi 70 cikin dari ga duniya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, “samar wa jama’a da zaman rayuwa mai dadi shi ne tushen ayyukanmu”, wanda ya shaida cewa, kawar da talauci da Sin ta cimma, babbar nasara ce da aka cimma ga duniya. Sin ta yi imani da yaki da talauci, kana tana da hanyoyin yaki da talauci. Tushen aikin daukar takamaiman matakai na yaki da talauci, shi ne neman dalilin da ya sa aka samu talaucin.

A hakika dai, yayin da Sin ta sa kaimi ga yaki da talauci a shekaru da dama da suka gabata, ta kiyaye yin kokarin taimakawa kasashe masu tasowa, wajen aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta MDD ta shekarar 2030. Bisa rahoton bankin duniya da aka gabatar, shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar, za ta taimakawa mutane miliyan 7 da dubu 600 wajen kawar da talauci mai tsanani, kuma mutane miliyan 32 za su kawar da matsakaicin talauci.

Bisa shirin da aka tsara, Sin za ta fara sabon aikin raya kasa ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkan fannoni a shekara mai zuwa, wannan ya bayyana cewa, kawar da talauci ba aiki ne na karshe ba, wato dai mafari ne na maida Sinawa su zama masu wadata tare. (Zainab)