logo

HAUSA

Kasar Sin tana kokarin yin kirkire-kirkire a cikin yanayin bude kofa

2020-12-28 21:01:59 CRI

Kasar Sin tana kokarin yin kirkire-kirkire a cikin yanayin bude kofa_fororder_微信图片_20201228210100

Sashen sauka na tauraron dan Adam na Chang'e-5, ya dawo da samfurin duniyar wata, kana na’urar karkashin ruwa ta "Fendouzhe" ta cimma nasarar yin nutso cikin teku mai zurfin mita 10,000, kamputa mafi sauri a duniya "Jiuzhang" ta fito, kuma tauraron dan Adam na Beidou ya gama aikin tsara tsarin sadarwar a duk fadin duniya… A shekarar 2020, wadda ta kasance shekarar da ake fuskantar manyan sauye-sauye da annobar COVID-19 a duniya, kasar Sin ta cimma nasarori da dama a fannin kimiyya da fasaha, wadanda suka baiwa duniya mamaki, wannan nasara ce mai wuyar samu.

Yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, bukatun cikin gida ne na kasar Sin, masu nasaba da neman ci gaban tattalin arzikinta mai inganci, kuma abu mai muhimmanci dake ingiza al'ummar kasar don shawo kan matsaloli.

Dangane da wannan shekarar da muke ciki kuwa, yayin da bangaranci da ra’ayin ba da kariya ke ci gaba da hauhawa a duniya, kasar Sin ta kara fahimtar cewa, ta hanyar karfafa binciken fasaha mai zaman kansa ne kawai za ta iya kaiwa ga matsayin jagoranci ta fuskokin fasaha da ci gaba, wanda hakan zai kai ga tabbatar da tsaron kasa gaba daya. 'Yancin fasaha da dogaro da kai, sun zama muhimman abubuwa masu goyon bayan ci gaban kasar.

Kasar Sin tana kokarin yin kirkire-kirkire a cikin yanayin bude kofa_fororder_微信图片_20201228210107

Ko shakka babu, kasar Sin ta ba da muhimmanci, da kuma jaddada yin kirkire-kirkire mai zaman kanta, wannan ba ya nufin tana rufe kofa, a maimakon haka, tana yin kirkire-kirkire bisa wani yanayi a bude. Kana kuma ta cika alkawarin da ta yi. A watan Yuni na shekarar 2020, an kammala jigilar tsarin tauraron dan Adam na Beidou-3 a duk fadin duniya. A yanzu haka, kasashen duniya fiye da rabi sun fara amfani da tsarin Beidou. Wannan masana'anta ta Beidou, da masana'antun da ke samar da hidimar da ta shafi hakan, za su karfafa ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban, tare da samar da sabuwar damar ci gaba. A watan Disamba na bana kuma, bayan na’urar bincike ta Chang'e 5 ta dawo da samfuran sinadaran wata, kasar Sin ta tabbatar da cewa, za ta raba samfuran tare da cibiyoyi, da masana a fannin kimiyya masu tunani iri daya na kasa da kasa, gami da bayanan binciken da suka dace don nazarin kimiyya, da zurfafa fahimtar dukkan bil'adama game da sararin samaniya.

Budewa na kawo cigaba, kuma kirkire-kirkire na haifar da makoma mai kyau. Kasar Sin da za ta shiga wani sabon mataki na ci gaba, za ta kara dogaro da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da karfafa ci gaba mai inganci, da samar da karin abubuwa masu daraja ga duniya, don inganta fitar da duniya daga cikin mawuyacin hali, da komawa hanyar ci gaba cikin sauri. (Bilkisu Xin)