logo

HAUSA

Wani shehun malami na kasar Kenya ya yaba wa manufar kasar Sin na kafa al’umma mai makomar bai daya

2020-12-28 14:34:30 CRI

Peter Kagwanja, shi ne shugaban cibiyar nazarin manufofin kasasahen Afirka ta kasar Kenya. Ya bayyanawa wakilin CMG a kwanakin baya cewa, manufar da kasar Sin ta gabatar, ta kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya, ta dace da moriyar kasashen Afirka, da ta kasar Sin. Kana tana da ma’ana sosai ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya.

Mista Peter Kagwanja ya ce, ya taba ziyartar kasar Sin har karo da yawa. Kana dalilin da ya sa haka, shi ne domin yana son fahimtar yanayin kasar Sin, da koyon dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su wajen raya kasa, wadanda za a iya yada su a nahiyar Afirka. Musamman ma fasahohin kasar Sin na fid da dimbin jama’arta daga kangin talauci cikin sauri. Ya ce,

“Cikin shekaru 40 bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ta fid da mutane kimanin miliyan 800 daga kangin talauci, inda ta kafa tarihi, da samar da gudunmowa ga aikin rage talauci na duniya. Sa’an nan na karanta littafin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa, Yin watsi da talauci, har karo da dama. Ta wannan littafi na samu fahimtar yadda kasar Sin ta yi amfani da manufar gyare-gyare da bude kofa wajen sanya wasu mutane daga cikin al’ummarta samun wadata, daga bisani wadannan mutane suka taimaki ragowar al’umma wajen fid da kansu daga talauci. Wadannan fasahohin sun amfani kasashenmu dake nahiyar Afirka matuka.”

A ganin mista Kagwanja, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin samun damar kawar da talauci, shi ne manufar kasar ta kokarin tabbatar da zaman karko da kwanciyar hankali. Ya ce, yanayin zaman karko ya sa ake samun ci gaban tattalin arziki, da baiwa mutanen kasar damar raya kasa ta wata hanya mai dorewa. Mista Kagwanja ya ce,

“Kasar Sin ta zama abin koyi ga sauran kasashe, a fannin raya kasa. Kana manufarta mafi muhimmanci, shi ne yadda take sanya burin kyautata zaman rayuwar jama’a. Wannan manufa ta sa ake samun damar kawar da talauci a kasar. Sa’an nan yadda aka kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali ya sa za a iya gudanar da wasu managartan manufofi cikin dogon lokaci. Kana tana iya daidaita manufofinta a kai a kai, don cimma burikan da ta sanya a gaba.”

Ban da wannan kuma, a cewar Kagwanja, tsare-tsare masu kyau sun sa kasar Sin ta iya shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri, da tabbatar da farfadowar tattalin arzikin kasar. Sa’an nan, bayan da kasar Sin ta samu nasara a fannin dakile cutar, kasar ta marawa kasashen Afirka baya sosai, wajen kandagarkin yaduwar cutar, lamarin da ya sa jama’ar kasashen ke matukar godiya, musamman ma ganin yadda kasar Sin ta yi alkawarin mai da allurar rigakafi a matsayin wani abun da zai amfanawa dukkan mutanen duniya. Ya ce,

“Shugaba Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin sun alkawarta cewa za a yi kokarin sanya kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa samun allurar rigakafin cutar COVID-19 da suke bukata, maganar da ta sanya mana farin ciki sosai. Yanzu muna kokarin shawo kan yaduwar cutar, sai dai har yanzu muna fuskantar yiwuwar sake barkewar annobar a karo na biyu ko na uku. Don haka muna dogaro kan hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a kokarinmu na tinkarar cutar COVID-19.”

Sa’an nan, yayin da yake magana kan batun kula da al’amuran duniya, Mista Kagwanja ya ce, kasashen Afirka da kasar Sin suna da wani ra’ayi na bai daya, na sanya bangarori daban daban zaman masu fada a ji a duniya. A ganinsa, wannan ra’ayi na da muhimmanci sosai, ta la’akari da yadda wasu kasashe ke kokarin aiwatar da manufar kashin kai.

“Kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da sauran kasashe ne, musamman ma domin kawar da ra’ayi na mulkin mallaka. Dukkan bangarorin Sin da na Afirka mun yarda da yin hakan. Wani babban jigon da za mu yi la’akari da shi a halin yanzu, shi ne ta yaya za a iya tabbatar da zaman lafiya a duniyarmu? Don amsa wannan tambaya, ya kamata mu gaggauta nazarin manufar da kasar Sin ta gabatar, ta kafa wata al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya.” (Bello Wang)

Bello