Shirin koyar da Sinawa mata ‘yan ci-rani fasahohin sana’o’i ya haskaka makomarsu
2020-12-28 14:56:41 CRI
A baya-bayan nan, Zhang Fuling ta fara zuwa makarantar koyon sana’o’i dake kusa da gidanta, inda take koyon dabarun da za su ba ta damar samun aiki a matsayin kwararriyar mai raino.
A baya, mazauniyar ta garin Songji, na gundumar Linquan ta lardin Anhui, ta kasance tana aikin ci rani a wani kamfanin samar da kayayyakin laturoni dake lardin Jiangsu.
Sai dai, annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan kamfanin, don haka Zhang ta koma gida tana laluben aiki. Wannan ne ya kai matar mai shekaru 50, fara zuwa ajin karbar horo da gwamnatin yankinsu ta shirya.
Yayin horon na kwanki 20, Zhang da sauran wasu mata 30, wasu daga cikinsu ‘yan ci-rani kamar ta, sun koyi yadda ake wa yara wasa da yi musu tausa da dafa musu abinci.
Da aka kammala horon, Zhang da sauran ‘yan uwanta mata sun rubuta jarrabawa, inda wadanda suka yi nasara, suka zama kwararru masu raino. “Da shaidar kwarewa, zan fi saukin samun aiki a bangaren”, cewarta.
Samar da horon sana’o’i ga ‘yan ci-rani, daya ne daga cikin matakai da dama da gwamnatin kasar Sin ke dauka a bana, da nufin bunkasa samar da ayyukan yi a tsakanin wasu rukunin mutane.
Yao Xiuping, mataimakiyar shugaban makarantar koyar da sana’o’i da Zhang ke zuwa, ta ce a matsayin gundumar da adadi mai yawa na mazaunanta ke zuwa ci-rani, Linquan na daukar batun bada horo da muhimmanci a matsayin wata hanya ta saukaka radadin annobar kan makomar ayyukan ‘yan ci-rani.
Za su iya shiga makarantu 7 da aka ware a gundumar, ciki har da ta Yao Xiuping, domin koyon sana’o’i daban-daban, kamar rainon yara da tsoffi da shirya furanni da kula da gida da sauransu.
Horon da ake yi kyauta a makarantar Yao, ya fara ne a watan Fabrairu. Da farko, ana yi ne ta kafar intanet saboda yaduwar COVID-19, amma tun cikin tsakiyar watan Mayu, aka koma yi a aji.
Kawo yanzu, sama da ‘yan ci-rani 3,000 ne suka karbi horon. “Daga cikin wadannan 3,000, kimanin 1,000 sun samu aiki nan take bayan kammala horon”, a cewar Yao.
Pang Shi, mataimakiyar daraktan sashen samar da aiki da sana’o’i da nazarin manufofi a kwalejin horas da jami’ai ta kasar Sin, ta ce abubuwa da dama, musammam annobar COVID-19, na barazana ga tattalin arzikin kasar Sin a bana. Lamarin dake nufin harkokin kasuwanci za su fuskanci matsaloli da dama.
“A irin wannan yanayi, wasu kamfanoni za su rage adadin ma’aikatan da za su dauka, hakan zai sa ‘yan ci-rani su sha wahalar samun aiki a bana”, a cewarta.
A watan Afrilun shekarar 2020, alkaluman hukumar kiddidiga ta kasar Sin, sun nuna cewa, kasar na da sama da ‘yan ci-rani miliyan 290 a bara, inda kaso 51 daga cikinsu ke aiki a bangaren bada hidima. Kaso 6.9 kuma na aiki a bangaren sufuri da masana’antar samar da kayayyaki, haka kuma, irin wannan adadi ne ke aiki a bangaren samar da masaukai da abinci.
“Ayyukan ‘yan ci-rani a wandannan bangarori biyu na cikin matsala saboda annobar COVID-19, kuma wasu mutane na fuskantar barazanar rasa ayyukan yi”, cewar Pang.
Shugaba Xi Jinping, ya sha nanata kira da a dauki matakan daidaita batun ayyukan ‘yan ci rani, yana mai karfafawa wadanda barazanar yaduwar annobar ba ta da yawa a yankunansu, su gaggauta komawa bakin aiki tare kuma da ba gwamnatoci kananan hukumomin umarnin kara kokarin yaki da fatara.
Wani rahoto da ma’aikatar kula da ayyukan gona da raya karkara ta kasar Sin ta fitar a watan Oktoba, ya nuna cewa, annobar ta tilastawa ‘yan ci-ranin da suka tafi garuruwansu domin hutun bikin bazara, zama a can na fiye da wata guda, lamarin da ya jinkirta musu neman aiki.
Bayan hutun bikin bazara mai muhimmanci ga kasar Sin, lokaci ne da ‘yan ci-rani ke neman sabbin ayyuka, sai dai, wasu sun koma gida saboda rashin samun aiki mai gamsarwa.
Babban masanin tattalin arziki na ma’aikatar Wei Baigang, ya ce sashen ya yi aiki tukuru domin bunkasa makoma da kudin shigar ‘yan ci-rani ta hanyar samar da guraben ayyukan yi a kan kari, da shirya baje kolin daukar ma’aikata, duk domin su ci gajiya, tare kuma da jigilar mutane zuwa wuraren aikinsu dake nesa da garuruwansu.
Matakan sun fara haifar da sakamako, a cewar Wei, zuwa karshen watan Satumba galibin ‘yan ci-ranin da annobar COVID-19 ta kawo wa tsaiko, sun samu aiki.
Zuwa karshen rubu’i na 3 na bana, adadin leburorin da suka bar kauyukansu domin neman aiki ya kai miliyan 179, wanda ya karu da miliyan 2 a kan na rubu’i na 2.
Haka kuma, ya ce matsakaicin kudin da ‘yan ci-rani ke samu a duk wata ya tashi daga yuan 4,035 (kwatankwacin dalar Amurka 617) inda ya karu da kaso 2.1.
A watan Oktoba, Zhang Ying, daraktar sashen samar da aiki na ma’aikatar kula da walwalar jama’a, ta yi jawabi yayin wani taron manema labarai a Beijing, inda ta ce “aikin ‘yan ci-rani na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankalin al’umma da inganta zamantakewarsu. Za mu yi iya kokarin ganin mun bullo da karin matakai da tabbatar da an aiwatar da su yadda ya kamata domin bada tabbacin samun aiki ga wadannan rukuni.”
Ta kara da cewa, annobar ta sanya samun aiki ga wasu ‘yan ci-rani a wajen garuruwa zama abu mai wahala, don haka ma’aikatar ta hada hannu da wasu sassan gwamnati 15 domin aiwatar da jerin matakan dake da nufin bunkasa damammakin samun aiki.
Ta ce yayin barkewar annobar, ma’aikatar ta kafa wasu tsaruka a matakan yankuna da larduna domin jigilar ‘yan ci-rani daga gidajensu zuwa kamfanoni, inda ta ce kawo yanzu tsarin ya taimakawa ‘yan ci rani miliyan 6 komawa bakin aiki a manyan birane.
Ta ce ma’aikatar ta bukaci ‘yan ci rani su nemi aiki a garuruwansu ko a wuraren dake kusa. Wannan zai ba wasu damar aiki a gida, maimakon yin doguwar tafiya.
A watan Afrilu, Luo Damei, mazauniyar gundumar Sangzhi ta lardin Hunan, ta samu aikin tsinkar ganyen shayi a wani kamfanim samar da ganyen shayi, da taimakon sashen kula da ma’aikata na yankin.
Kafin barkewar COVID-19, matar mai shekaru 60 ta yi aiki a wata masaka dake lardin Fujian har na tsawon shekaru 9, inda take samun Yuan 6,000 zuwa 8,000 a ko wane wata.
A bana, annobar ta sa odar da ake ba kamfanin ta ragu, lamarin da ya sa aka dauki mutane kalilan sannan kuma albashin ba yawa.
Bisa la’akari da shekarunta da kuma yadda matasa za su fi ta saurin samun aiki saboda yadda takara ta karu a bana, sai Luo ta yi amfani da shawarar da jami’an yankin suka bayar na neman aiki a kusa da gida.
A shekarun baya-bayan nan, kamfanin sarrafa ganyen shayi na gundumar Sangzhi na samun ci gaba cikin sauri, wanda ya haifar da neman karin ma’aikata, don haka Luo ta yi saurin samun aiki.
Ta kan fara aiki da karfe 6 na safe, ta tashi da misalin 7 na dare. Tana samun hutun sa’o’i 2 ko 3 da rana. Ana biyanta Yuan 14 kan kilo daya na ganyen shayin da ta tsinko. A haka, ta kan samu a kalla Yuan 2,000 a wata.
Mijinta da suke aiki tare a Fujian, yanzu yana aikin gini a kusa da gidansu, inda yake samun Yuan 2,500 duk wata.
Idan aka hada kudin da dukkansu ke samu, bai kai wanda suke samu lokacin da suke ci-rani ba, amma duk da haka, Luo ta gamsu.
A cewarta, “kudin da nake samu yanzu ba laifi, duba da yadda bana ta zo daban. Kuma, tafiyar mintoci kalilan zan yi daga gida zuwa wurin aikina, sannan tsadar rayuwa ba ta kai ta Fujian ba”.
“Baya ga haka, ba yarinya nake zama ba, makudan kudaden da ake biyana saboda aiki tukuru a wani gari ba zai dawwama ba. lokacin dawowa gida ya yi.”(Kande Gao)