logo

HAUSA

Cinikayyar Sin da ketare ta yanar gizo ta yi matukar bunkasa a bana

2020-12-28 19:37:56 CRI

Cinikayyar Sin da ketare ta yanar gizo ta yi matukar bunkasa a bana_fororder_11

Biyo bayan jerin matakan da hukumomin kasar Sin ke cigaba da dauka domin bunkasa fannin tattalin arziki da hada hadar cinikayya a cikin gida da kuma ketare, alamu sun tabbatar da cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu. Ko shakka babu, wadannan matakan sun taka gagarumar rawa wajen bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da sauran sassa na duniya. Alal misali, rahotanni daga lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin na cewa, lardin wanda ke matsayin cibiyar hada-hadar cinikayyar waje a gabashin kasar, ya samu bunkasar cinikayyar ketare ta yanar gizo cikin watanni 11 na farkon wannan shekarar.

Yawan hajojin da aka fitar ketare daga lardin ta cinikayyar yanar gizo tsakanin wannan watanni 11 sun kai na kudin Sin yuan biliyan 91.16 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 13.95, adadin da ya karu da kaso 28.9 cikin dari a shekara guda, kamar yadda sashen lura da cinikayyar lardin ya bayyana. Bugu da kari, adadin hajojin sayayyar daidaikun mutane da aka yi cinikayyar su tsakanin lardin da kasashen ketare ta yanar gizo, sun karu da kaso 33.4 bisa dari, inda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 33.9, wanda hakan ya haifarwa lardin karuwar makin hajojin da ake shigarwa da kaso 1.2 bisa dari. Yanzu haka dai lardin Zhejiang, ya kafa sabbin cikakkun yankunan gwaji na cinikayyar hajojin da ake fitarwa ketare har guda 7, wadanda suka hada da na Wenzhou, da Shaoxing, da Huzhou, da Jiaxing. Sauran su ne na Quzhou, da Taizhou da kuma Lishui.

Mahukuntan lardin dai na kira ga kananan hukumomin da aikin ya shafa da su tsara dabarun tallafawa manufar. A cewar daraktan sashen lura da cinikayyar waje ta lardin Sheng Qiuping, mahukuntan lardin na Zhejiang sun sha alwashin samar da karin kyakkyawan yanayi, da ingantattun hidimomi, na bunkasa hada hadar cinikayyar waje ta yanar gizo. Lallai wannan al’amari ya kasance wani labari mai faranta rai ga kasar Sin da kasa da kasa musamman a wannan halin da ake ciki na karayar tattalin arzikin duniya a sanadiyyar barkewar annobar COVID-19.(Ahmad Fagam)