logo

HAUSA

An taya dakarun Sin da suka kammala aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu murna

2020-12-28 21:10:51 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya taya dakarun sojin Sin na rukuni na 6 da su kammala aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu murnar kammala aikin su cikin nasara.

Kwanan baya, dakarun sun dawo gida, bayan da suka kamala aikinsu. Kafin hakan rukunin dakarun ya mika ragamar aiki ga tawagar da za ta maye gurbinsa kasar.

Da yake amsa tambaya game da wannan batu, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, Zhao Lijian ya ce, a bana ake cika shekaru 30, tun bayan da kasar Sin ta fara shiga ayyukan MDD na wanzar da zaman lafiya. Kuma daga shekarar 1990 zuwa yau, Sin ta tura rukunonin sojinta zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD har karo 26, inda karkashin hakan ta aike da dakaru sama da 40,000, domin taimakawa irin wadannan ayyuka.

Jami’in ya ce hakan ya sanya Sin zama kasa mafi yawan tura dakarun wanzar da zaman lafiya, tsakanin dukkanin kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin tsaron MDD. Zhao Lijian ya kara da cewa, cikin shekaru sama da 30 da suka gabata, tawagogin Sinawa masu aikin wanzar da zaman lafiya sun taka muhimmiyar rawa, wajen bunkasa zaman lafiya, da karfafa gwiwar al’ummun dake fuskantar tashe tashen hankula.

Ya ce Sin har kullum za ta ci gaba da aiwatar da alkawuranta na taimakawa matakan wanzar da zaman lafiya a duniya, za ta kuma zama babbar mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya, da wanzar da doka da oda a matakin kasa da kasa. (Saminu)