logo

HAUSA

Budewar kasar Sin na bayar da kwarin gwiwa wajen farfado da tattalin arzikin duniya

2020-12-27 16:45:51 CRI

Budewar kasar Sin na bayar da kwarin gwiwa wajen farfado da tattalin arzikin duniya_fororder_微信图片_20201227164454

"Me ya sa duniya ke bukatar kasar Sin?" Wannan shi ne batun dake kumshe cikin jawabin da wani dan Amurke mai yada bidiyo a yanar gizo Cyrus Janssen ya yi a wata jami'ar kasar Canada a kwanan baya, a yayin jawabinsa, Cyrus Janssen ya jaddada muhimmancin kasar Sin ga duniya daga fannonin mahangar kasuwa, budewa, da kimiyya da fasaha da dai sauransu, ya kuma nuna cewa, ra’ayin kasar Sin na bude kofa da hadin kai shi ne abin da al'ummar yau ke bukata. Bayan an loda wannan bidiyon a dandalin sada zumunci na yanar gizo ta kasar Amurka, ya samu karbuwa sosai daga wajen masu amfani da yanar gizo.

"A sanya kasuwar Sin ta zama kasuwar duniya", wannan ita ce damar kai tsaye da kasar Sin mai budewa ke kawo wa duniya. Daga rage farashin harajin kayayyakin da take shigowa da yawansu ya kai iri 850, zuwa rage lokacin kwastam gaba daya don shigo da kayayyaki, da kuma zuwa ci gaba da gudanar da bikin baje kolin hada hadar cinikayya na Guangzhou, da bikin baje kolin ba da hidimar cinikayyya, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na duniya na kasar Sin, da kuma baje kolin Sin-ASEAN da dai sauransu, kasuwar kasar Sin mai yawan al’ummomi biliyan 1.4 tana ta samun makoma mai kyau, wadda kuma ke kara biyan bukatun kasashe daban daban.

Budewar kasar Sin na bayar da kwarin gwiwa wajen farfado da tattalin arzikin duniya_fororder_微信图片_20201227164503

A matsayinta na muhimmin bangare na tsarin masana'antu na duniya, kasar Sin ta jagoranci sake dawo da aiki da samar da kayayyaki bayan ta shawo kan annobar COVID-19 yadda ya kamata, wanda hakan ta kiyaye zaman daidaito na tsarin masana'antu da na samar da kayayyaki yadda ya kamata. "Lokacin da aka kunna inji a masana'antun kasar Sin, tsarin masana'antun duniya zai tabbata." Wannan ya zama ra’ayin bai daya da kamfanonin kasashen waje masu yawa suka cimma. Jaridar Nikkei ta kasar Japan ta ce, ana ta kara samun alamar cewa, tattalin arzikin duniya na kara dogaro da kasar Sin.

A lokaci guda, a yayin da ake raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" mai inganci da kuma inganta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya shiyya, kasar Sin ta himmatu sosai wajen kirkirar ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na duniya da inganta tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya, hakan ya nuna nauyin dake kanta a matsayinta na babbar kasar ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya. "Za mu hada gwiwa tare da dukkan kasashe, yankuna da kamfanonin da suke son yin hadin gwiwa da kasar Sin." Wannan yana nufin cewa, huldar tattalin arziki a tsakanin Sin da duniya za ta kai zuwa wani sabon matsayi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)