logo

HAUSA

CMG da gwamnatin yankin musamman na Macao sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare

2020-12-27 16:57:12 CRI

CMG da gwamnatin yankin musamman na Macao sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare_fororder_微信图片_20201227154537

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG da gwamnatin yankin musamman na Macao sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a Macao a jiya Asabar. Jami’in farko na gwamnatin yankin musamman na Macao Ho Iat Seng, da shugaban CMG Shen Haixiong da dai sauransu sun halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar.

A cikin ’yan shekarun baya, CMG da gwamnatin yankin musamman na Macao sun gudanar da hadin gwiwa sosai wajen samar da labarai, watsa shirye-shiryen wasannin motsa jiki, da shirye-shiryen fina-finai da na talabijin, da na yawon shakatawa da kuma na raya al'adu. Domin fadada fannonin hadin gwiwa, da sanya tsarin hadin gwiwa ya zama yadda ya kamata, kana da inganta bunkasuwar yankin Macao a nan gaba. Bangarorin biyu sun yanke shawarar sanya hannu kan "Yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin CMG da gwamnatin yankin musamman na Macao”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)