logo

HAUSA

An bude sabon babi na hadin gwiwar Sin da Afirka kan shawarar “Ziri daya da hanya daya”

2020-12-27 20:19:13 CRI

An bude sabon babi na hadin gwiwar Sin da Afirka kan shawarar “Ziri daya da hanya daya”_fororder_微信图片_20201227191216

Kwanan baya, kasar Sin da kungiyar tarayyar Afirka (AU) sun rattaba hannu kan "Shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar Sin da kungiyar tarayyar Afirka kan inganta shawarar ‘Ziri daya da Hanya da daya’", wanda zai inganta yadda ya kamata game da zurfafa hadewar shawarar din ta "Ziri daya da Hanya daya" da kuma ajandar kungiyar AU ta shekarar 2063. Hakan zai taimaka wajen inganta bukatar juna tsakanin bangarorin biyu, da magance kalubalen da duk duniya ke fuskanta tare, shirin da ya bude wani sabon babi ga hadin gwiwar Sin da Afirka ta raya shawarar "Ziri daya da Hanya daya".

Shirin hadin gwiwar shi ne takardar hadin gwiwa ta farko da kasar Sin ta sanya hannu tare da wata kungiyar kasa da kasa don raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ya yi bincike mai matukar amfani kan hadewar ayyukan raya shawarar da manyan tsare-tsaren ci gaba na yankuna daban daban da shawarar ta shafa. Wanda ya ba da misali mai muhimmanci ga hadin gwiwa mai inganci a tsakanin Sin da abokanta na duniya wajen raya shawarar ta "Ziri daya da hanya daya", zai kuma samar da sabbin damammaki na hadin gwiwar duniya da kara sabon karfi ga samu bunkasuwa tare.

An bude sabon babi na hadin gwiwar Sin da Afirka kan shawarar “Ziri daya da hanya daya”_fororder_微信图片_20201227191226

Bisa shirin hadin gwiwar kuma, kasar Sin da kwamitin kungiyar tarayyar Afirka za su kafa tsarin daidaita ayyukan raya shawarar, da warware matsalolin da aka samu yayin aiwatar da shirin ta hanyar tsarin shawarwari da tuntubar juna mai kyau. Wannan zai taimaka wa kasar Sin da kasashen Afirka wajen kara gano wurare mafiya dacewa da hadin kai dake karkashin manufofinsu a yayin da suke kokarin cimma burinsu na neman bunkasuwa. Baya ga ci gaba da zurfafa fannonin hadin kai na gargajiya da suka shafi manyan ababen more rayuwa, samar da kayayyaki da dai sauransu, Sin da Afirka na iya fadada sabbin wuraren hadin gwiwa a fannoni kamar zaman rayuwar jama’a, samun ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da makamantansu, kana da kara zurfafa hakikanin hadin kai a fannoni daban daban.

Wannan annobar COVID-19 wacce har yanzu ake fuskanta ta sake nuna gaskiyar dogaro da juna tsakanin kasashe daban daban, da kuma makomar bai daya ta dan Adam. Kasar Sin ta sha bayyana niyyarta na hada kai tare da kawayenta, ciki har da Afirka, don raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" da za ta kasance hanyar tinkarar kalubale tare, da kiyaye lafiyar mutane, da farfado da tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Bilkisu Xin)