logo

HAUSA

Akwai bukatar hadin-kan kasa da kasa domin tinkarar yaduwar sabbin nau’o’in kwayar cutar COVID-19

2020-12-26 19:25:40 CRI

Akwai bukatar hadin-kan kasa da kasa domin tinkarar yaduwar sabbin nau’o’in kwayar cutar COVID-19_fororder_AA

Duk da cewa kasashen duniya na ci gaba da kokarin gudanar da nazari da samar da allurar riga-kafin annobar COVID-19, amma abun damuwa shi ne, kwanan nan Birtaniya ta sanar da gano wani sabon nau’in kwayar cutar a kasar, har ma yana bazuwa cikin saurin gaske zuwa wasu kasashe, ciki har da Denmark, da Holland, da Italiya, da Belgium, da Isra’ila, da Singapore, da Australiya da sauransu. Bugu da kari, Afirka ta Kudu da Portugal da Ecuador sun ce su ma sun gano wani sabon nau’in kwayar cutar, wanda ya bambanta da wadda aka gano a Birtaniya.

A Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, an ce an gano wani sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 wanda ya bambanta da wadanda aka gano a Birtaniya da Afirka ta Kudu. A cewar darekta janar na cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka ko kuma Africa CDC a takaice, Mista John Nkengasong, wannan sabon nau’in kwayar cutar yana da saurin yaduwa, amma ba’a tabbatar ko za ta kara haifar da illa ga lafiyar dan Adam ba.

Akwai bukatar hadin-kan kasa da kasa domin tinkarar yaduwar sabbin nau’o’in kwayar cutar COVID-19_fororder_BB

A daidai wannan lokaci da ake kokarin ganin bayan annobar a duniya, musamman hana yaduwarta tsakanin kasa da kasa, ana kara bukatar hadin-kan kasashen duniya maimakon samun rarrabuwar kawuna. A nata bangare, kasar Sin tana himmatuwa wajen nazari gami da samar da allurar riga-kafin cutar gami da maganinta, har ma ta riga ta fara baiwa wasu kasashe allurar. Amma akwai wasu ’yan siyasar kasashen yamma, wadanda suka yi ikirarin cewa, wai wannan allura “diflomasiyyar allurar riga-kafi” ce da kasar Sin ta yi, da nufin fadada tasirinta a fagen siyasar duniya. Ko shakka babu, saka batun siyasa cikin aikin dakile yaduwar cutar, zai illata hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da yaduwar cutar.

Tun farkon bullar cutar, akwai wasu ‘yan siyasar kasashen yamma wadanda suka yi ikirarin cewa wai kasar Sin ce ta kirkiri kwayar cutar, daga bisani lokacin da kasar take kokarin samarwa kasashe daban-daban abubuwan rufe baki da hanci kyauta, ko kuma a halin yanzu da take rarrabawa duniya allurar riga-kafin da ta samar, wasu mutane suna cewa wai “diflomasiyyar abun rufe baki da hanci” ko “diflomasiyyar allurar riga-kafi”, wadannan maganganu ne masu ban dariya kwarai da gaske. Gaskiyar magana ita ce, inganta hadin-gwiwa da mu’amala tare da sauran kasashe da kasar Sin take yi a fannin dakile yaduwar cutar, babu wani buri ko kuma sharadin siyasa ko moriyar tattalin arziki a cikinsa. Abin farin ciki shi ne, yanzu haka akwai wasu kasashe wadanda suka riga suka amince da fara amfani da allurar riga-kafin da kasar Sin ta samar musu, al’amarin da ya nuna cewa allurar riga-kafin kasar Sin na da inganci da tsaro, kana, har kullum kasar Sin tana gudanar da harkokinta daidai bisa doka da ka’idojin kasa da kasa.

A yayin da wasu kasashe ke fuskantar babbar barazanar yaduwar sabbin nau’o’in kwayar cutar COVID-19, abun da ya kamata kasa da kasa su yi shi ne zama tsintsiya madaurinki daya, maimakon a rura wutar rikici ko kuma yada jita-jita kan wasu kasashe, saboda abun da ya ci doma ba ya barin awe. (Murtala Zhang)