logo

HAUSA

MDD ta aika dakarun wanzar da zaman lafiya daga Sudan ta kudu zuwa CAR gabanin zaben kasar

2020-12-25 10:34:24 CRI

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, MDDr ta fara tura dakarun wanzar da zaman lafiya daga kasar Sudan ta kudu zuwa jamhuriyar Afrika ta tsakiya CAR, domin taimakawa aikin wanzar da zaman lafiya a CAR gabanin zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar dokokin kasar dake tafe a ranar Lahadi.

A ranar Laraba ne kwamitin sulhun MDD ya amincewa bukatar da babban sakataren MDDr Antonio Guterres ya gabatar na neman tura dakarun tsaron, domin su gudanar da aiki na tsawon watanni biyu, wanda ya kunshi bataliya biyu na kwararrun sojoji, da kuma wasu jiragen yakin sojoji biyu daga ofishin shirin wanzar da zaman lafiya na MDDr dake Sudan ta kudu domin su tallafawa dakarun kiyaye zaman lafiyar MDD dake jamhuriyar Afrika ta tsakiya CAR, a cewar Stephane Dujarric, kakakin Guterres.

Jami’in ya bayyana cewa, an tura dakarun ne domin karawa dakarun wanzar da zaman lafiyar dake aiki a CAR karfi, wacce aka fi sani da MINUSCA.

Game da batun tsaro kuwa, Dujarric ya ce, dakarun kiyaye zaman lafiyar za su ci gaba da aikin dakile karuwar barazanar kungiyoyin ‘yan bindiga a CAR.(Ahmad)