logo

HAUSA

IMF: Ana sa ran Sin za ta kara yin tasiri a fannin tinkarar kalubalen tattalin arzikin da duniya ke fuskanta

2020-12-25 14:54:04 CRI

Babban wakilin asusun ba da lamunin duniya na IMF da ke kasar Sin Steven Alan Barnett ya bayyana a kwanan baya, cewar ya yi wa kasar Sin matukar godiya saboda ta samar wa asusunsa kudi, domin rage basussukan da ke kan kasashe matalauta. Ban da wannan kuma asusun na sa ran Sin za ta taka muhimmiyar rawa a fannin tinkarar kalubaben tattalin arzikin da duniya take fuskanta, sakamakon bullar cutar COVID-19. A ganinsa, Sin na da kwarewa wajen fito da kyakkyawan tsarin cinikayyar kasa da kasa mai adalci da salon bude kofa da martaba ka’ida, bisa hadin gwiwa tare da sauran abokan cinikayyarta.

Steven Alan Barnett, babban wakilin asusun ba da lamunin duniya na IMF da ke kasar Sin ya furta yayin wani kwas din horas da kwalejin nazarin kimiyyar kasafin kudi ta kasar Sin ta shirya, cewar sakamakon bullar cutar COVID-19, tattalin arzikin duniya a shekarar bana yana fuskantar tabarbarewa mafi tsanani, tun bayan babbar tawayar tattalin arzikin duniya da ta faru tsakanin shekarar 1929 zuwa ta 1933. Bisa hasashen da asusun IMF ya yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2020, mutane kimanin miliyan 80 zuwa 90 za su sake komawa kangin talauci sakamakon annobar. A kokarin tinkarar illar da annobar ta yi wa tattalin arziki, kasashe daban daban sun fito matakai. Barnett ya nuna cewa, karin kananan kasafin kudi da hanyoyin tara kudaden shiga da ake fito da su a kasashen da suka ci gaba ya kai kaso 9.3 na GDPn su. Hakika ba a taba ganin irin wanan mataki ba. Yana mai cewa,

“Wannan ne karo na farko da aka yi haka a tarihi. Gaskiya ba a taba ganin kasashe masu ci gaba sun fito da matakan kudi da yawa irin haka don farfado da tattalin arzikinsu ba. Game da kasashe masu tasowa ma, wannan adadi ya kai kaso 3.6 na GDPn su, gaskiya sun yi kokari sosai. Ban da wannan kuma, gwamnatocin kasashe daban daban sun sanar da samar da rancen kudi da ba da tabbacin rancen kudi don nuna goyon baya.”

Barnett ya kuma nuna cewa, hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen kawar da illar da annobar ta yi wa tattalin arziki. Ya kara da cewa, tun bayan bullar annobar, asusun IMF ya fito da shirye-shiryen taimako fiye da 80, a kokarin taimaka wa kasashe daban daban wajen sassauta matsin da tattalin arzikinsu ya shiga. Kasashe masu karamin karfi 49 sun samu taimakon asusun, 29 daga cikinsu kuwa aka soke ko rage basussukan da yake bin su. Barnett ya godewa kasar Sin kan yada amfaninta a cikin aikin.

“Kasar Sin tana daya daga cikin mambobinmu da suka samar da kudade don rage ko soke basussukan da ke kan kasashe mafiya fama da talauci. Don haka muna mata godiya sosai.”

Hasashen da asusun IMF ya yi a watan Oktoba, ya nuna cewa, tattalin arzikin duniya a bana, zai ragu da kaso 4.4 bisa dari. Amma kasar Sin ita ce kasa daya tak da ta samu karuwar tattalin arziki a bana a duk fadin duniya, wadda adadin karuwar zai kai kaso 1.9 bisa na bara.

A nasa bangaren, Li Xin, mataimakin Mr. Barnett na ganin cewa, a fannin hadin kan kasa da kasa don yaki da cutar COVID-19, kasar Sin ta shiga shirin samarwa da ma rarraba allurar rigakafin cutar da ke karkashin jagorancin hukumar kiwon lafiyar duniya WHO, baya ga sa hannu cikin “Shawarar dakatar da biyan bashi” da “Tsarin daidaita basussuka baki daya” da kungiyar G20 ta tsarawa kasashe marasa karfi. Li Xin ya ce, yana fatan Sin za ta kara taka rawa wajen tinkarar kalubalen tattalin arzikin da duniya take fuskanta. Ya ce,

“Kasar Sin na iya ci gaba da samar da kudade don raya muhimman ayyukan more rayuwar al’ummar duniya, a kokarin taimaka wa sauran kasashe wajen tinkarar illar da annobar ta dade tana yi wa tattalin arzikinsu. Sauyin yanayi zai ci gaba da addabar duniya. Mun kuma lura da cewa, Sin ta gabatar da babban burin dakatar da fitar da hayakin carbon-dioxide nan da shekarar 2060, hakika muna yaba mata matuka a kan wannan. Bugu da kari, duk da yanayin siyasa da tattalin arziki mai sarkakiya da duniya ke fama da shi, ya kara nuna kwarewar kasar Sin wajen yin kokari tare da sauran abokan cinikayyarta wajen fito da kyakkyawan tsarin cinikayya mai adalci da salon bude kofa da ma martaba ka’ida sosai.”(Kande Gao)