logo

HAUSA

MUZGUNAWA KAMFANONIN SIN DAKE AMURKA ZAI CI GABA DA ILLATA MORIYAR KASASHEN BIYU

2020-12-24 20:48:11 CRI

Har yanzu dai, ga alama mahukuntan Amurka ba su yi watsi da manufofin su na yiwa kamfanonin Sin dake gudanar da hada hada bisa doka a Amurka matsin lamba ba, domin kuwa a baya bayan nan ma, shugaban kasar dake daf da sauka daga mulkin Donald Trump, ya sanya hannu kan wata doka da ta tanaji tursasawa kamfanonin Sin dake Amurkan bin wasu dokokin hukumar lura da hada hadar hannayen jarin kasar, irin dokokin da a baya suka shafi kamfanonin kasar Amurkan su kadai.

Masharhanta da dama na kallon wannan mataki a matsayin kokarin dakile ci gaban kamfanonin Sin dake samun tagomashi a Amurka, musamman ganin cewa, ba wannan ne karo na farko da Amurkan ke kakabawa kamfanonin Sin tarnaki, da ka’idojin tsaurara harkokinsu a cikin kasar Amurkan ba.

Masana a fannin tattalin arziki kuwa, na ganin irin wadannan matakai na sanya wasu kamfanonin Sin dake Amurka shiga matsi, wanda kan haifar da hasara ko faduwa, ba kawai ga masu mallakarsu ba, har ma masu zuba jari Amurkawa dake morar riba daga musamman kanana da matsakaitan kamfanonin na Sin. Baya ga asarar haraji da guraben ayyukan yi da hakan ka iya haifarwa.

Wani bangare da mahukuntan na Amurka ke fakewa da shi wajen kafa sharudda masu tsauri ga kamfanonin Sin dake Amurka shi ne fannin tsaron kasa, to amma idan an kalli wannan fanni da kyau, za a ga mafi yawan dalilai masu nasaba da hakan ba su da madogara ta zahiri, illa dai kawai dabarun siyasantar da harkar tsaro da jami’an Amurkan suka jima suna yi.

Dalili kan hakan shi ne, yadda a baya bayan nan mahukuntan Amurkan suka sanyawa wasu kamfanonin Sin, da wasu jami’an Jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar takunkumi, wanda hakan zai shafi yanayin gudanar da harkokin wasu kamfanonin Sin da dama. Bangaren Amurkan ya zargi kamfanonin na Sin da ta’ammali da wasu ’yan siyasar Sin wadanda Amurkar ke cewa suna taimakawa wajen saba ka’idojin siyasa da Amurka ke bi. Amma abun tambaya a nan shi ne, wace dokar kasa da kasa ce ta baiwa Amurka damar ware mutanen da wani kamfanin waje zai yi mu’amala da su? Kuma yaushe ne Amurka ta zama malamar koyar da salon mulki? Kana shin anya kuwa salon Dimokaradiyyar da Amurkar ke tutiya da shi ya kai kasar “Tudun mun tsira”?

Sanin kowa ne dai cewa, a halin da ake ciki a yanzu, mahukuntan Amurkan sun gaza shawo kan manyan matsalolin dake addabar kasar ta fuskar kiwon lafiya, inda kasar ta zama ta farko a duniya, wajen yawan mutanen da cutar numfashi ta COVID-19 ta hallaka. Wannan kadai ya isa misali na gazawar gwamnatin Amurka mai ci, kuma maimakon ta maida hankali ga muhimman batutuwan dake gabanta, sai ga shi jagororin ta, suna ta bullo da matakai na kara gurgunta sashen cinikayya da raya tattalin arzikin kasar.

Ko shakka babu, a wannan gaba da duniya ke fuskantar tarin kalubale, musamman mai nasaba da bazuwar cutar COVID-19, ake kuma ta fafutukar farfado da tattalin arzikin duniya, lokaci ne mafi dacewa da manyan kasashen duniya za su kara rungumar hadin kai da tafiya tare, da kaucewa rura wutar sabani, da haddasa yanayin da zai kai ga fito na fito.

Tarihi ya riga ya shaida yadda irin wannan yanayi ke kaiwa, ta yadda a duk lokacin da Amurka ta bullo da matakan muzhunawa Sin, ita ma Sin na mayar da martani bakin gwargwado, daga karshe kuma al’ummun sassan biyu da fannin ya shafa, ke dandana mummuman tasirin hakan.

Daga karshe idan mun yi duba da yadda Sin ta kasance babbar kasa daya tilo a duniya, da ta samu bunkasar tattalin arziki a bana, yayin da manyan kasashen duniya ciki hadda Amurka, ke kokarin fita daga yanayin matsi da annobar COVID-19 ta haifar, ba abun da ya dace ga Amurka, illa ta shiga taitayin ta, ta yi watsi da siyasantar da alakar ta da sauran kasashe, ko a kai ga “Gudu tare a tsira tare”. Bahaushe dai na cewa, “Duk dan da ya hana uwarsa barci, shi ma ba zai rintsa ba!” (Saminu Hassan)

Saminu