logo

HAUSA

Amurka za ta girbi abun da ta shuka

2020-12-24 20:37:12 CRI

 

Amurka za ta girbi abun da ta shuka_fororder_微信图片_20201224203519

Sakawa sauran kasashe takunkumi, mataki ne da Amurka ta kan dauka ba gaira ba dalili. Shekarun baya-bayan nan, sanya takunkumi ya zama wata alama ta wasu ’yan siyasa marasa imani, dake yunkurin sarrafa harkokin kasar.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce tun kafuwar gwamnatin Amurka mai ci a shekarar 2017, ta kaddamar da matakan sanya takunkumi fiye da sau 3900, wato kimanin sau 3 ke nan a kowace rana. Kasashen da take kakabawa takunkumin sun hadda da abokanta a tarihi, da abokan gaba, da ma kasashen dake yin takara da ita.

Dalilin da ya sa Amurka ta fi son irin wannan mataki shi ne, sanya takunkumin ya fi aiwatar da matakan soja araha. To amma, idan ya zama wata gwamnati ba ta da sauran wani mataki na daidaita dangantakar diplomasiyyar ta da sauran sassa illa kakaba takunkumi, hakan na nuna cewa ba ta da isashen karfin daidaita banbancin ra’ayi.

Amurka za ta girbi abun da ta shuka_fororder_微信图片_20201224203507

A sa’i daya kuma, sauran kasashe za su yi biris da wannan mataki, duba da cewa, babu wata dabara ta daban da Amurka za ta aiwatar, illa dai za ta girbi abin da ta shuka.

A halin yanzu, kamata ya yi kasashe daban-daban, manya ko kanana, su rungumi matsayin daidaito da mutunta juna. Mataki mafi dacewa wajen daidaita bambancin ra’ayi shi ne, sulhuntawa da gudanar da shawarwari. Takunkumi da ake kakabawa, na da alaka da mutunci, abun alfahari ne, daidai da muradu kowace kasa, kuma ba wata kasa mai ikon mulkin kai da za ta mika wuyanta.

Irin wadannan matakan da ’yan siyasar Amurka suke dauka ba su da amfani, wajen daidaita matsalolin da ake fuskanta, za su kuma mayar da ita saniyar ware a duniya. (Amina Xu)