logo

HAUSA

Gülmire Atihan ta cimma burinta na samun wadata a kauyen Baixituogelake dake jihar Xinjiang

2020-12-24 13:35:29 CRI

Gülmire Atihan ta cimma burinta na samun wadata a kauyen Baixituogelake dake jihar Xinjiang

Gundumar Shule tana arewa maso yammacin yankin Kashgar na jihar Xinjiang ta kasar Sin, kuma wurin ciyayi a yankin ya kai kaso 5.6 bisa dari, a don haka ta taba fama da kangin talauci matuka, a shekarar 2017, malamar Sinanci a makarantar koyar da fasaha ta yankin Kashgar ‘yar kabilar Uygur Gülmire Atihan ta je kauyen Baixituogelake domin gudanar da aikin kyautata rayuwar mazauna wurin bisa kiran da gwamnatin jihar ta yi.

Aikin kyautata rayuwar al’umma ta hanyar kara fahimtar yanayin da suke ciki, mataki ne da jihar Xinjiang ta dauka tun daga shekarar 2014, makasudin daukar matakin shi ne, domin taimakawa al’ummar jihar dake fama da kangin talauci, an zabi jami’ai daga hukumomin gwamnati a matakai daban daban a fadin jihar domin su je aiki a kauyuka.

A lokacin da Gülmire Atihan ta je kauyen Baixituogelake a shekarar 2017, ta ga iyalai 67 dake kunshi mutane 245 dake cikin daukacin iyalai 344 dake kunshi mutane 1531 suna fama da talauci mai tsanani, Gülmire Atihan ta waiwaye ta gaya mana cewa, “An haife ni ne bayan shekarar 1980, wato lokacin da aka samu ci gaban tattalin arzikin kasar cikin sauri, saboda an fara yin kwaskwarima da kuma bude kofa ga ketare, shi ya sa muke jin dadin rayuwa matuka, amma lokacin da na zo kauyen, na ga manoman yankin dake kudancin jihar Xinjiang suna fama da talauci kuma suna kwana ne a cikin gidaje marasa inganci.”

To ta yaya za a canja tsohon tunaninsu? Gülmire Atihan ta dauka cewa, ya dace a wayar musu da kai tare kuma da koyar da su hanyar samun wadata, sai Gülmire Atihan wadda aka nada a matsayin mataimakiyar shugabar tagawar aikin kyautata rayuwar al’umma ta tattaunawa da kwamitin kauyen, daga baya sun tsai da kuduri cewa, za su kafa wata makarantar dare ga manoman kauyen, ta yadda za su daga inganta tunaninsu, ban da haka, sun yanke shawara cewa, abu mafi muhimmanci shi ne, su kara mai da hankali kan aikin gina kauye mai kyau, saboda sun ga kura tana tashi ta ko ina a kauyen, yawancin manoman kauyen suna rayuwa ne a gidaje marasa inganci, kuma babu manyan gine-ginen more rayuwar jama’a na zamani a kauyen, Gülmire Atihan ta yi mana bayani cewa, “Mun sha kiran taruka a kauyen, domin tattauna yadda za a gudanar da ayyukan da suka shafi muradunmu na kyautata muhallin kauyenmu, alal misali yadda ake sarrafa shara ko bola, da yadda ake gyara titunan kauyan, da yadda ake kyautata muhallin rayuwar manoman kauyen, to, domin cimma wannan burin, da farko, mun yi kokarin yada manufofin da abin ya shafa ga manoma a makarantar dare a ranakun Litinin da Laraba na kowane mako, inda muka nuna musu muhimmancin gina kauye mai tsabta, haka kuma mun yi musu jagora kan yadda za su shiga aikin yadda ya kamata, a mataki na biyu kuwa, mun fara tsara shirin gyara gidajen kwanansu, ta hanyar raba wurarensu na rayuwa da kiwon dabbobi da kuma dasa ‘ya’yan itatuwa, a sa’i daya kuma, mun fi mai da hankali kan aikin gyara ban daki da dakin dafa abinci.”

Bayan shekaru biyu, sun samu sakamako a bayyane, ba ma kawai muhallin rayuwar manoman kauyen ya kyautata ba, har ma kudin shigarsu ya karu matuka.

Ya zuwa shekarar 2018, an mayar da kauyen Baixituogelake kauyen ba da misali wajen kyautata muhallin rayuwa a gundumar Shule, a karshen shekarar kuma, daukacin manoman kauyen sun fita daga kangin talauci, abu mafi faranta ran mutane shi ne, ya zuwa karshen shekarar 2019, an kammala aikin gyara dukkan gidajen kwana na iyalai 361 dake kauyen.

A halin yanzu, idan ka je kauyen Baixituogelake, ko ina za ka ga gidaje masu inganci, da ‘ya’yan itatuwa masu kamshi a farfajiyar gidajen kwanansu, da titunan zamani, da wuraren sarrafa bola na zamani.

Gülmire Atihan ita ma ta yi farin ciki matuka, lokacin da ta ga manyan sauye-sauyen da suka faru a kauyen, tana mai cewa, “A baya manoman kauyenmu suna kwana ne a cikin tsoffin gidaje marasa inganci, yanzu haka suna rayuwa a cikin gidajen kwana na zamani, inda aka saka gado da teburin cin abinci da doguwar kujera da teburin karatu da sauransu, muhallin rayuwarsu shi ma ya kyautata, suna kuma cike da sabon burin na kara kyautata rayuwarsu.”(Jamila)