logo

HAUSA

Kwamitin kolin JKS wadda ke mulkin kasar Sin ya shirya taron bunkasa tattalin arziki a shekarar 2021

2020-12-23 14:47:31 CRI

A kwanakin baya ne kasar Sin ta gudanar da babban taronta na tattalin arziki. Taron wanda Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin na JKS kana shugaban kasar ya jagoranta ya bayyana cewa, kasar za ta mayar da hankali wajen kara karfi a fannin kimiya da fasahar kirkire-kirkire a shekarar 2021, a wani mataki na magance manyan kalubale dake kawo cikas ga ci gaban kasar da ma fannin tsaro.

Kwamitin kolin JKS wadda ke mulkin kasar Sin ya shirya taron bunkasa tattalin arziki a shekarar 2021

Haka kuma a shekarar ta 2021, kasar Sin za ta kara mayar da hankali wajen fadada bukatun na cikin gida, da kara samar da ayyukan yi, da fadada rukunin matsakaitan masu samun kudin shiga, da hanzarta samar da makoma ta bai daya. Sauran fannonin sun hada da, karfafa yaki da yin babakere da dakile yadda ake fadada kasuwannin hannayen jari barkatai.

Taron ya kuma bayyana bukatar a fito da wani tsari na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli nan da shekarar 2030, da tsara sabbin hanyoyin, da ci gaba da yin aiki tukuru don kandagarki da hana fitar da hayaki dake illa ga muhalli.

kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya kananan sana’o’i da neman bunkasuwa mai dorewa a shekarar 2021, da kara zurfafa gyare-gyare da bude kofa a dukkan fannoni.

Kwamitin kolin JKS wadda ke mulkin kasar Sin ya shirya taron bunkasa tattalin arziki a shekarar 2021

Taron ya kara da cewa, idan har kasa tana son samun ci gaba, wajibi ne, ta aiwatar da gyare-gyare da kara bude kofa. kasar Sin za ta warware matsalar irin shuka da filayen noma, da kara karfinta na tabbatar da samar da hatsi da muhimman kayayyakin noma.

A cewar taron, kasar Sin za ta yi aiki tukuru, don tabbatar da cewa, tattalin arzikinta na tafiya kan turbar da ta dace. A cewar sanarwar bayan taron, shugabannin kasar Sin sun tsara taswirar raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2021. Duk da tasirin annobar COVID-19, kasar Sin ce kadai a duniya, tattalin arzikinta zai bunkasa a bana, kamar yadda hukumomi hada-hadar kudi na duniya suka bayyana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)