logo

HAUSA

Sin na fatan yayata gina tsarin sufuri na kasa da kasa domin ci gajiyar bai daya

2020-12-23 21:03:16 CRI

A baya bayan nan ne aka budewa ababen hawa, sashen babbar hanyar Sukkur-Multan ta yankin Peshawar-Karachi na kasar Pakistan. Bude wannan babbar hanya shi ne aiki mafi girma a fannin samar da ababen more rayuwa da aka gudanar, karkashin tsarin inganta hadin gwiwar raya tattalin arziki tsakanin Sin da Pakistan.

Hanyar wadda kamfanin kasar Sin ya gina, ta rage tsawon tafiya tsakanin Sukkur da Multan, daga sa’o’i 11 zuwa kusan sa’o’i 4 kacal.

Sin na fatan yayata gina tsarin sufuri na kasa da kasa domin ci gajiyar bai daya

Wannan dai manuniya ce game da matsayin Sin na bunkasa gina makomar bil Adama ta bai daya a fannin sufuri. Kamar dai yadda aka bayyana ciki wata takardar bayani ta gwamnatin kasar Sin wadda aka fitar a ranar Talata, mai lakabin "Manufar wanzar da ci gaba mai dorewa ta Sin a fannin sufuri", Sin na aiwatar da kudurin MDD na nan da shekarar 2030, game da ajandar wanzar da ci gaba mai dorewa. Kaza lika Sin na aiki tukuru a fannin ba da jagoranci a fannin sufuri a matakin kasa da kasa, tana kuma karfafa musaya da hadin gwiwar sassan kasa da kasa a wannan fanni.

"Idan ana son arziki, wajibi a fara da gina hanya." Wannan salon magana na Sinawa, na nuni ga tabbas da ababen more rayuwa na sufuri ke bayarwa, wajen raya tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma. Ya zuwa karshen shekarar 2019, adadin tsayin titunan kasar Sin ya kai kilomita 139,000, wanda hakan ya sanya kasar zama ta daya a duniya a wannan fanni. Bisa kididdiga, tsayin manyan hanyoyin kasar ya kai kilomita miliyan 5.013, ciki hadda na tagwayen hanyoyi da suka kai kilomita 150,000, wanda a nan ma kasar ta Sin ta zamo ta daya a duniya. Har ila yau, tsayin sassan hanyoyi masu gadoji, da wadanda ke bi ta cikin duwatsu ko tsaunuka da ake ginawa, da wadanda ake amfani da su, shi ma dai ya kai matsayin farko a duniya.

Takardar bayanin ta ci gaba da lasafta irin wadannan ayyuka da kasar Sin ke kan gaba cikinsu a tsakanin sauran sassan duniya, wanda hakan ke nuna cewa, Sin ta zama zakaran gwajin dafi, idan dai ana batu na tsarin samar da hanyoyi masu inganci, tana kuma ci gaba da zage damtse, wajen zama tashar harkokin sufuri ta duniya.

Sin na fatan yayata gina tsarin sufuri na kasa da kasa domin ci gajiyar bai daya

A matsayin ta na babbar kasa mai lura, yayin da take fadada ayyukan gina ababen more rayuwa a gida, Sin na kuma ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya a fannin raya sufuri, tana kara ingiza ci gaban sufuri a matakin kasa da kasa da raya tattalin arziki.

A matsayin ta na kasa dake goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, Sin na ci gaba da ingiza ayyukan sauye sauye a fannin jagorancin sufurin kasa da kasa. Takardar bayanan ta kuma nuna yadda har kullum, Sin ke tsayawa kan gaskiya, wajen sauke nauyin dake wuyanta a mataki na kasa dasa, tana kara fadada "Da’irar abokanta" don kara bude sashen sufuri da hadin gwiwa, tare da bada muhimmiyar gudummawa ga yaki da fatara na duniya, da kandagarkin gurbatar muhalli, da ci gaban tattalin arziki. Musaman a wannan shekara ta fama da annoba, Sin ta yi rawar gani wajen tabbatar da an wanzar da sufurin kayayyakin tallafi da ake bukata na yaki da cutar COVID-19, wanda hakan ya yi matukar amfani wajen bunkasa hadin gwiwar sassan kasa da kasa, a yakin da ake yi da cutar, da kuma fannin farfado da tattalin arziki.

Abu ne a zahiri, cewa Sin dake ci gaba da rungumar akidar samar da ci gaban al’umma, za ta dore wajen bunkasa ababen more rayuwa na sufuri masu inganci, tare da yayata manufar hade dukkanin sassan duniya waje guda a fannin na sufuri. (Saminu Hassan)