logo

HAUSA

An gano sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 a Afirka ta kudu

2020-12-23 13:32:35 CRI

A kwanakin baya ne aka gano sabon nau’in kwayar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Birtaniya, lamarin da ya janyo hankalin al’ummun kasa da kasa matuka, yanzu haka kasar Afirka ta kudu ita ma ta sanar da cewa, ta gano sabon nau’in kwayar cutar, daga baya jami’ar hukumar kiwon lafiya ta duniya Maria D. Van Kerkhove ta gaskanta cewa, sabon nau’in kwayar cutar da aka gano a Afirka ta kudu ba ta da nasaba da sabon nau’in kwayar cutar da aka gano a Birtaniya, amma dukkansu suna yaduwa tsakanin mutane cikin sauri.

Kwanan baya masana da jami’an kiwon lafiya na kasar Afirka ta kudu sun sanar cewa, sun gano wani sabon nau’in kwayar cutar numfashi ta COVID-19 da aka bata sunan “501.V2”, kuma a ranar 21 ga wata, jami’ar hukumar kiwon lafiya ta duniya dake kula da fasahar aikin gaggawa Maria D. Van Kerkhove ta gaskanta cewa, sabon nau’in kwayar cutar da aka gano a Afirka ta kudu bata da nasaba da sabuwar nau’in kwayar cutar da aka gano a Birtaniya, tana mai cewa, “Yanzu an gano wani sabon nau’in kwayar cutar numfashi ta COVID-19 a Afirka ta kudu, duk da cewa, ta yi kama da kwayar cutar samfurin 501, kuma suna yaduwa ne a lokaci guda, amma akwai bambanci tsakaninta da sabon nau’in da aka gano a Birtaniya, hukumomin da abin ya shafa na Afirka ta kudu sun riga sun gabatar da sakamakon binciken da suka samu bisa mataki na farko ga hukumar kiwon lafiya ta duniya.”

Bisa rahoton binciken da Afirka ta kudu ta gabatar wa hukumar lafiya ta duniya, an lura cewa, masanan tawagar binciken dake karkashin jagorancin cibiyar KRISP ta kasar sun gano sabon nau’in kwayar cutar bayan da suka tantance samfuran kwayar cutar da suka samu a cikin watanni biyu da suka gabata, kuma sun lura cewa, sabon nau’in kwayar cutar shi ma yana yaduwa tsakanin mutane cikin sauri, masanan Afirka ta kudu suna ganin cewa, wata kila wannan sabon nau’in kwayar cutar ya haifar da sake barkewar annobar cutar a kasar ta Afirka ta kudu a karo na biyu, shugabar kungiyar likitocin kasar Angelique Coetzee ta bayyana cewa, “Sabon nau’in kwayar cutar numfashi ta COVID-19 da aka gano a Afirka ta kudu yana kawo babbar illa ga lafiyar jikin mutanen da suka kamu da cutar, kuma akwai babbar wahala wajen jinyar su, tun daga tsakiyar watan Nuwamban da ya gabata, masanan Afirka ta kudu sun yi bincike kan samfuran kwayar cutar, daga baya sun tarar da wannan sabon nau’in kwayar cutar a cikin samfuran da yawansu ya kai kaso 90 bisa dari, ana iya cewa, sabon nau’in kwayar cutar yana yaduwa cikin sauri matuka, wannan shi ma dalili ne da ya sa annobar cutar ta barke a karo na biyu a Afirka ta kudu, har ta fi tsanani bisa karo na farko.”

Angelique Coetzee ta kara cewa, sabon nau’in kwayar cutar da aka gano a Afirka ta kudu zai jefa matasa da mutane masu karfi cikin yanayi mai tsanani, tana mai cewa, “A lokacin barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a karo na farko ko kuma yanzu, mutane wadanda suke fama da cututtuka iri daban daban kamar su karin sukari cikin jini, ko karin kiba cikin jini, su kan shiga yanayi mai tsanani, amma yanzu sabon nau’in kwayar cutar da ya bullo ya harfar da sabuwar matsala gare mu, wato matasa wadanda ba su fiya kamuwa da cutar cikin sauki ba suna iya kamuwa da cutar cikin sauri a yanzu, wannan shi ne dalilin da yasa mun ga tsoffafi wadanda ke fama da cututtuka iri daban daban, tare kuma da matasa a cikin dakunan jinyar marasa lafiya masu tsanani.”

Tun bayan da Afirka ta kudu ta sanar cewa, ta gano sabon nau’in kwayar cutar, sai nan take kasashen Faransa da Isra’ila da Turkiya da Jamus da Saudiya Arabiya da Switzerland da Mauritius da sauransu sun hana fasinjojin da suka fita daga kasar Afirka ta kudu su shiga kasashensu, kuma sun dakatar da jirga-jirgar jiragen sama dake tsakaninsu da kasar.

Ministan kiwon lafiya na Afirka ta kudu Zweli Mkhize ya bayyana cewa, duk da cewa, ana damuwa da bullowar sabon nau’in kwayar cutar, amma bai kamata a ji tsoro ba.

Ya zuwa yammacin ranar 21 ga wata, agogon kasar Afirka ta kudu, gaba daya adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai dubu 930 da 711, kuma adadin mutanen da suka rasu sakamakon cutar ya kai dubu 24 da 907, kana sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin ayoyi 24 da suka gabata sun kai 8789.(Jamila)