logo

HAUSA

Murna na kokarin komawa ciki

2020-12-23 17:26:56 CRI

Murna na kokarin komawa ciki

Yayin da duniya ke murnar samun alluran riga kafin annobar COVID-19, matakin da ake fatan zai kawo karshen matsalar da annobar ta haifarwa duniya, sai ga shi kwayar cutar COVID-19 na kara bazuwa cikin sauri a Burtaniya har ma da Afirka ta kudu, al’amarin dake damun al’umma kwarai da gaske. Wai bakon da ake cewa ya tafi, ashe ya labe a bayan gari.

Yanzu haka gwamnatin Burtaniya, tana gudanar da bincike kan ko saurin yaduwar cutar na da wata alaka da wani sabon nau’in kwayar cutar, har ma ta daga matsayin kandagarkin yaduwar cutar daga mataki na uku zuwa na hudu a wasu sassa, ciki har da birnin London, da kudu maso gabashin Ingila da wasu yankunan dake gabashin kasar.

Tun a ranar 14 ga wannan wata na Disamba ne, gwamnatin Birtaniya ta sanar da gano sabon nau’in kwayar cutar, wanda ake kira “VUI-202012/01”. Kawo yanzu babu shaidun dake nuna cewa, ko wannan sabon nau’in cutar, zai kara haifar da mace-mace, ko kuma zai yi mummunan tasiri kan allurar riga kafi gami da maganin cutar da aka fara amfani da su a wasu sassa na duniya ciki har da Burtaniyar. Kwararru da masana suna himmatuwa wajen gudanar da nazari don tabbatar da hakan.

Rahotanni na cewa, gwamnatocin kasashen Jamus da Faransa da Ireland da Holland da Italiya da Austria da Luxemburg da makamantansu, sun sanar da haramta shigar fasinjoji da ma jiragen sama daga Birtaniya cikin kasashensu,domin hana yaduwar cutar. Riga kafi aka ce ya fi magani.

A don haka masana na cewa, kamata ya yi mahukunatan Burtaniya su yi koyi da kasar Sin, wajen sanar da sauran kasashe da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin lafiya muhimman bayanai game da wannan sabon nau’in kwayar cutar, kar duniya da sake fadawa wani hali.

A halin da ake ciki yanzu, yayin da wasu kasashe suka fara jarraba alluran rigakafin COVID-19 da aka fara samarwa, a hannu guda kuma kasar Sin, tana fatan samar da riga kafi mai inganci da araha wadda duniya, musamman kasashe masu tasowa za su fara amfana da shi.

Kafin wannan kuma, mahukuntan kasar Sin sun gayyaci masana daga hukumar lafiya ta duniya(WHO) da su ziyarci kasar, don kara gano asalin kwayar cutar da ma matakan da suka dace a kara dauka, don ganinbayanwannanannoba nan da nan.

Masu sharhi na cewa, wajibi ne a koma ga batun da mahukuntan kasar Sin ke ta yin kira a kai, wato yin hadin gwiwa don magance duk wata matsala da ka iya kunno kai, kafin wankin hula ya kai mu dare. Hannu daya,ba ya daukar jinka. (Ibrahim Yaya)