logo

HAUSA

Hadin gwiwa a bangaren makamashi yana amfanawa kasar Sin da sauran kasashe

2020-12-23 21:02:59 CRI

Hadin gwiwa a bangaren makamashi yana amfanawa kasar Sin da sauran kasashe

Kowa ya san cewa a kan kalli takardar tsabar kudi a matsayin “katin kasuwanci” na wata kasa. Sai dai a kasar Guinea dake nahiyar Afirka, a kan takardar tsabar kudinta mafi daraja ta Franc dubu 20, akwai wani zane na babbar madatsar ruwa mai samar da wutar lantarki ta Kaleta, wadda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina ta.

Hakika a lokacin da aka fara samar da takardar tsabar kudin, ba a kammala aikin gina madatsar ruwan ba tukuna. Amma hakan ya nuna yadda jama’ar kasar Guniea suke dora cikakken muhimmanci kan madatsar ruwan, da yadda suke yin Allah-Allah ganin kammalar aikin gina ta.

Yanzu abun da mutanen kasar Guinea suke nema ya tabbata. A shekarar 2015, madatsar ruwa ta Kaleta ta fara samar da wutar lantarki, daga bisani an samu daidaita matsalar karancin wutar lantarki a birnin Conakry, fadar mulkin kasar Guinea, gami da kyautata zaman rayuwar jama’ar da suke zaune a kewayen birnin. Yanzu haka da dare, jama’ar wurin su kan taru a wasu filayen da ake samun hasken fitila, ko kuma kallon shirin telabijin na gasannin kwallon kafa, maimakon hawan gado tun da wuri.

Madatsar ruwa ta Kaleta, wani misali ne kan yadda kasar Sin take kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a fannin aikin makamashi. Bisa wata takardar bayani da kasar Sin ta gabatar a ranar Litinin da ta gabata, dangane da yadda ake raya aikin makamashi a kasar, an ce kasar Sin ta riga ta fara yin hadin gwiwa tare da kasashe da yankuna fiye da dari daya, a fannonin cinikin makamashi, da zuba jari, da samar da kayayyaki da na’urorin da ake bukata, da sabunta fasahohi, da dai makamantansu. Inda kasar ke samar da karin gudunmowa a fannin samar da makamashi mai tsabta, don kare muhallin duniya.

Dalilin da ya sa ake iya samun wannan ci gaba a kasar Sin, shi ne domin kasar tana matukar kokari a fannin nazarin sabbin fasahohi masu alaka da makamashi. Cikin shekarun da suka gabata, kasar ta ba mutanen duniya mamaki, bisa yadda take kokarin sauya salon makamashinta zuwa masu tsabta. Yanzu haka, ana samun kasuwa mafi girma ta makamashin da ake iya sabunta su a kasar Sin, kana tana samar da mafi yawan na’urori masu samar da makamashi mai tsabta.

A fannin kera na’urori masu samar da wutar lantarki ta zafin rana, kasar Sin tana samar da na’urori masu inganci, gami da sayar da su zuwa kasashe da yankuna fiye da 200. A fannin hada injuna masu samar da wutar lantarki mai aiki da karfin iska kuma, yawan injunan da ake hada su a kasar Sin ya kai kashi 41% na daukacin injunan da ake samar da su a duniya. Wadannan nasarorin da aka samu, suna taimakawa kasar Sin fitar da na’urorin da ta hada zuwa sauran kasashe.

Ya kamata a lura da cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana tsayawa kan manufar amfanar juna, yayin da take kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe, a fannin makamashi. Madatsar ruwa ta Kaleta ta sa an samu hasken fitilu a Conakry, kana tashar samar da wutar lantarki ta zafin rana da aka gina a Kaposvar dake kasar Hungary ta sa ana samun raguwar fitar da iska mai dumama yanayi da ta kai ton dubu 120 a kowace shekara. Yayin da wani shiri na yin amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki a Dubai na kasar UAE, zai iya samar da makamashi mai tsabta ga magidanta dubu 320.

Wadannan manyan gine-gine, da kayayyakin more rayuwa da kamfanonin Sin suka gina, suna taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma burin da jama’ar wadannan kasashe suka sanya gaba, na neman raya kasa, da ci gaban al’umma. (Bello Wang)

Bello