logo

HAUSA

Abubakar Bello Rafindadi dalibin Najeriya dake karantar bangaren titin jirgin kasa a kasar Sin

2020-12-22 15:57:17 CRI

Abubakar Bello Rafindadi dalibin Najeriya dake karantar bangaren titin jirgin kasa a kasar Sin

Kasar Sin da tarayyar Najeriya suna gudanar da hadin-gwiwa a bangarori da dama, kuma bangaren layin dogo na daya daga cikinsu, musamman layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna wanda shahararren kamfanin kasar Sin mai kula da harkokin gine-gine wato CCECC ya bada taimakon shimfidawa. Domin taimakawa mutanen Najeriya kara samun kwarewa a fannin zirga-zirgar jiragen kasa, kamfanin CCECC ya samowa wasu ‘yan kasar hanyar zuwa kasar Sin domin karanta ilimin a jami’ar Chang’an dake birnin Xi’an, Abubakar Bello Rafindadi na daya daga cikinsu.

Abubakar Bello Rafindadi dalibin Najeriya dake karantar bangaren titin jirgin kasa a kasar Sin

A zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar Bello Rafindadi, dan asalin jihar Katsina ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin zirga-zirgar jiragen kasa, kuma wannan shi ne babban dalilin da ya sa ya kudiri aniyar zuwa kasar don yin karatu, saboda yana son bada gudummawa ga hadin-gwiwar Sin da Najeriya a fannin zirga-zirgar jiragen kasa. Abubakar Bello ya kuma bayyana bambancin yanayin karatu tsakanin kasarsa da kasar Sin, da fahimtarsa kan rayuwar al’ummar kasar Sin da ma ci gaban da kasar ta samu a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)