logo

HAUSA

Makiyayan Yankin Hainan Na Lardin Qinghai Suna Kan Hanyar Samun Wadata

2020-12-22 14:24:56 CRI

Makiyayan Yankin Hainan Na Lardin Qinghai Suna Kan Hanyar Samun Wadata

Makiyayi Ren Qingtai yana jin farin ciki, bayan da a kwanakin baya, saniyarsa wadda ake kula da ita a yankin kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho na kauyen Saishitang ta haihu, Ren Qingtai mai shekaru 34 ya yi matukar farin ciki, yana mai cewa, sabo da manufofi masu kyau, rayuwarsu tana ci gaba da samun kyautatuwa.

Cikin sansanin gwaji na kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho, akwai jerin gidajen shanu da aka gina, inda ake kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho sama da dari 6. A kan fitar da shanu daga gidajensu tun da misalin karfe 7 da safe, domin zuwa yin kiwo a yankin ciyayi, sa’an nan, a dawo da su da karfe 12 na rana, domin su huta.

Irin wannan hanyar kiwon shanu ta ba su damar yin yawo a babban yankin ciyayi, kuma ba za su bata yankin ciyayi sosai ba, wannan shi ne, hanyar kiwon shanu da aka dukufa wajen ingantawa a kauyen Saishitang domin daidaita kiwon dabbobi da kare muhalli.

Kauyen Saishitang yana garin Wenquan na gundumar Xinghai dake yankin Hainan na kabilar Zang mai cin gashin kansa dake lardin Qinghai na kasar Sin, kauyen na da nisan kilomita 70 daga gundumar, kuma kwatankwacin tsayinsa ya kai mita dubu hudu, gaba daya akwai iyalai 569 dake zaune a wannan kauye, inda ke kunshe da mutane 2186, cikin wadannan iyalai, akwai masu fama da talauci guda 80, da suka kunshi mutane 311. Sabo da karancin albarkatun kasa mai inganci a wannan kauye, ba a shuka kayan noma a kauyen, manoma da makiyaya dake wurin, su kan sami kudin shiga ta hanyar kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho da ragunan Zang.

Ren Qingtai ya ce, a da, makiyaya su kan sami kudin shiga ta hanyar sayar da madara da gashin raguna, kudin shiga da iyalinsa da ya kunshi mutane 4 ya samu bai wuce dubu 10 a shekara daya.

Wannan ya sa, an shigar da iyalin Ren Qingtai cikin jerin masu fama da talauci a shekarar 2017.

Sa’an nan a shekarar 2018, shi da iyalinsa, sun kaura daga wani yankin tsauni mai nisa zuwa gidajen da gwamnatin ta kebe musu a kauyen Saishitang. Baya ga yadda wurin zamansu ya samu kyautatuwa, abu mafi farin ciki gare su shi ne, sun koyi sabbin fasahohin kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho.

Bayan da suka kaura zuwa kauyen Saishitang, Ren Qingtai ya shigar da yankin ciyayi na gidansa cikin kamfanin hadin gwiwa, ta yadda, kwamitin kauyen zai kula da yankin ciyayi baki daya, kuma Ren Qingtai ya fara yin aikin kiwon shanu a sansanin gwaji na kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho domin kwarewa a wannan fanni, sa’an nan, uwargidansa da yaransa su ma sun fara aiki a sansanin, lamarin da ya kyautata zaman rayuwarsu kwarai da gaske.

Ren Qingtai ya ce, bayan da suka fara aiki a sansanin gwaji na kiwon shanu, ko wane wata, suna samun kudin shiga kimanin Yuan dubu 6, wato kusan dubu Yuan 70 a ko wace shekara, adadin da ya ninka sosai idan aka kwatanta da lokacin baya.

Jiu Xijie shi ne darektan farko na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Saishitang, a shekarar 2015, ya kai ziyara gidajen mutanen kauyen domin jin shawarwarinsu game da yadda za a kawar da talauci, sa’an nan, ya kafa kamfanin hadin gwiwa a kauyen, da sansanin gwaji na kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho, ta yadda, masu fama da talauci, za su samu riba a wace shekara ta hanyar kiwon shanu da raguna.

Bayan shafe shekaru da dama suna kokari, mutanen kauyen sun samu karin kudin shiga, Jiu Xijie ya ce, a watan da ya gabata, sun sayar da shanu masu dogon gashi da manyan kaho sama da dari daya, hakan ya sa, ya zuwa karshen bana, ko wane iyali dake kauyen zai samu kudin shiga da ya kai Yuan dubu 3.

Jin Cuojie ya taba yin aiki a waje, yanzu ya komo kauyensu domin yin aiki a sansanin gwaji na kiwon shanu masu dogon gashi da manyan kaho, a ko wace shekara, yana samun kudin shiga kimanin Yuan dubu 40.

Ya ce, “Duk da cewa ba ni da shanu da yawa, amma na samu kudin shiga da yawa, kuma muna samun riba wajen kiwon shanu a kauyenmu, kudin shigarmu ya karu matuka. Yanzu, muna da aiki mai kyau, kuma ko wace rana, ina komawa gidana bayan na kammala aiki, ban taba zaton zan iya rayuwa kamar haka ba.”

Cikin ‘yan shekarun nan, gundumar Xinghai tana yin amfani da wata hanyar neman bukasuwa cikin hadin gwiwa tsakanin kamfanoni da kamfanonin hadin gwiwa da manona, domin ba da taimako wajen raya kamfanonin aikin gona da kamfanonin hadin gwiwa na sana’a. Ta kuma tsara wasu hanyoyin neman bunkasuwa domin kawar da dukkanin manoma da makiyaya na gundumar daga kangin talauci.

Yanzu, an samu wata hanyar raya aikin kiwon shanu a kauyen Saishitang, kuma ba tare da bata muhalli ba, lamarin da ya tabbatar da ci gaban kauyen bisa fasaha da kimiyya kamar yadda ake bukata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)