logo

HAUSA

Yadda Amurka Ke Tafka Manyan Karaireyi Da Yadda Take Yakar COVID-19

2020-12-21 22:08:13 CRI

“Ba zan taba boye komai ba, mun samu nasara! Kalaman da babban jami’in lafiya na jami’ar kula da harkokin lafiya dake kudancin California ta Amurka Brad Spellberg ya bayyana kwatsam yayin wata zantawa da kafar wata kafar watsa labarai. A cewar kafar CNN, a cikin makon da ya gabata, an samu karuwar barkewar annobar COVID-19 a California, yawan wadanda ake kwantarwa ya fi karfin asibitin, ma’aikatan lafiya suna fuskantar matsin lamba.

Yadda Amurka Ke Tafka Manyan Karaireyi Da Yadda Take Yakar COVID-19

Lamarin ba wai California ya kusan gurguntawa ba, abin ya shafi baki dayan Amurka. Kafar watsa labaran ABC ta bayyana a ranar 19 ga wata cewa, kwanaki bakwai din da suka gabata, sun kasance mako mafi muni, tun lokacin da annobar ta barke a Amurka. Bisa kiyasi, a kowa ce rana, ana samun sama da sabbin mutane 210,000 da suke kamuwa da cutar, baya ga mutane 18,000 kuma da cutar take halakawa.

Abin takaici shi ne, da wuya a zargi ‘yan siyasar Amurka wadanda suka shafe tsawon watanni suna karyar dakile yaduwar cutar. A ‘yan kwanakin da suka gabata, shafin intanet na Amurka dake wallafa bayanan abubuwan dake faruwa na yau da kullum, mai suna “Political Facts” ya zabo, tare da yin rikon sakainar kashi da ma karyata sabuwar cutar mura” a matsayin karyar shekarar 2020 da ya saba tabkawa a kowa ce shekara. Dalili kuwa shi ne, karya mafi muni ba kawai illa ba ce, amma yadda take halaka jama’a.

A ranar 19 ga wata, jaridar “Washington Post” ta walafa wani sharhi mai kunshe da kalmomi dubu goma mai taken “abubuwan dake faruwa: kin amincewa da gaskiya, facaka, tunanin shugabannin Amurka ya sa annobar zama hunturu mafi hadari” inda sharhin ya bayyana abubuwan da suka faru cikin watanni 10 da suka gabata, kuskuren da gwamnatin Amurka ta tabka daya bayan daya.

Yadda Amurka Ke Tafka Manyan Karaireyi Da Yadda Take Yakar COVID-19

Koda yake, sabanin haka, gwamnatin Amurka mai ci, tana barazanar yin fito na fito da sauran kasashen duniya, inda take ci gaba da janyo hankalin kasashen duniya. A daya hannun kuma, ba ta yin komai a cikin gida game da dakile yaduwar cutar, ko sanar da duniya abubuwan dake faruwa a cikin kasar game da annobar, hakan ya sa duniya kara fahimtar ra’ayi na son kai da ‘yan siyasar Amurka ke dauka kan wannan annoba.

A bangaren Amurkawa kuwa, ya kamata su fahimci cewa, har yanzu fa ba shiga lokacin hunturu ba. A cewar cibiyar dake bayani kan alkaluman da suka shafi lafiya da tantacewa ta jami’ar Washignton,  sama da Amurkawa 237,000 za su mutu daga sabuwar cutar mura a cikin watanni uku masu zuwa. Tambayar a nan ita ce, yaushe ne, bala’in da dan-Adam ya haddasa” za ta ci gaba da kasancewa a Amurka. Amma kuma abin kunya ne da bakin ciki ga kasar da ke daukar kanta ta daya kuma mai karfin fada aji a duniya. (Ibrahim Yaya)