logo

HAUSA

Buaka Mukoko Ephrem: Matasan Sinawa Na Da Himmar Raya Kwallon Kafa

2020-12-20 21:28:40 CRI

Buaka Mukoko Ephrem: Matasan Sinawa Na Da Himmar Raya Kwallon Kafa

 

Yayin da kasashen duniya ke kara rungumar wasannin motsa jiki, a matsayin hanyar nishadantarwa da kuma kara inganta lafiyar jiki, sanin kowa ne cewa, kwallon kafa na kan gaba a jerin wasanni mafiya farin jini a duniya. A yanzu haka, kwallon kafa na kara samun karbuwa tsakanin matasa da yara kanana a kasar Sin.

Buaka Mukoko Ephrem, matashi ne dan asalin kasar Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo wanda ke da shekaru 30 a duniya, tuni kuma ya fara haskawa a fannin horas da yara kanana wasan kwallo a nan kasar Sin.

Yayin wata tattaunawa da manema labarai, Mr. Ephrem ya jinjinawa kwazon matasan Sinawa, a fannin raya wasan kwallon kafa da neman kwarewa. Yana mai cewa ko shakka ba bu, matasan Sinawa na kara gogewa sannu a hankali.

Ya ce cikin shekaru 5 da suka gabata, Sin ta samu ci gaba a fannoni da dama, musamman fannin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, wanda hakan ya samar da damammakin bunkasuwa ga kawayen ta ‘yan sauran kasashen waje dake aiki a Sin.

Kafin zuwan sa kasar Sin, Buaka Mukoko Ephrem, ya taba taka leda a gida cikin kungiyar ‘yan kwallo matasa, kana bayan shigowarsa kasar Sin shekaru 8 da suka gabata, ya kuduri aniyar buga kwallo a tawagar ‘yan wasa kwararru. Sai dai a cewar sa hakan ba ta samu ba, amma duk da haka abubuwa masu kyau sun faru gare shi.

Buaka Mukoko Ephrem: Matasan Sinawa Na Da Himmar Raya Kwallon Kafa

Ya ce "A gida na buga wasa tare da tawagar ‘yan wasa matasa tun ina dan shekaru 16. Amma ban samu wasu kudade masu yawa ba. A lokacin ina da wani aboki Basine, wanda ya ce min ina ga ya dace ka zo kasar Sin don gwada sa’ar ka. A lokacin sai na yanke shawarar tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Chongqing Lifan, amma sai kocin kungiyar ya shaida min cewa, yana son ‘yan wasa ne da suka taba buga kwallo a wasu kungiyoyin kasar Sin. Duk da haka ban kahura ba. Ba zan koma gida ba."

Daga baya, yayin da yake karatu a Guangzhou, Ephrem ya rika buga wasa a kananan kungiyoyin kwallon kafa dake birnin, yana kuma aikin tafinta na yaren Faransanci. A shekarar 2014, ya yi nasarar samun takardar shaidai zama mai horas da ‘yan wasa kwallon kafa. A shekarar 2017 kuma, Ephrem wanda ke amsa sunan Sinanci na “Xiaolong”, ya fara aikin koci a hukumance a birnin Guangzhou.

Game da hakan “Xiaolong” ya ce aiki a Sin ya fi dadi, duk da cewa akwai wahala, amma ina yi iya dariya."

Cikin shekarun da ya kwashe yana wannan aiki, tauraruwar “Xiaolong” na ta kara haskawa, yana aiki kusan sa’oi 8 a duk rana a filin kwallo, in ban da ranar Litinin.

Ya ce "Na fara da yara ‘yan shekaru 3 da masu shekaru 4, sai kuma ‘yan shekaru 6, sai 7. Daga baya na fara horas da matasa masu shekaru 10 da masu 12. A yanzu ina koyar da masu shekaru 16 da wasu kadan masu shekaru 18. Yanzu na zama mai horas da kwallo. Ina da buri. Dole ne na yi iyakacin kokari na."

Game da gudummawar wannan matashin koci dan asalin Afirka, daya daga iyayen yara da yake koyarwa ya bayyana cewa, ajujuwan da Ephrem ke koyarwa suna da matakan horo masu yawa, kuma dalibansa na koyon sabbin abubuwa da dama. Ya ce koci ne mai kwarewa, yana kuma da saukin hali, don haka iyayen yaran da yake horaswa suke jinjina masa kwarai, kuma har daga kungiyar guangzhou Evergrande star ana tura masa yara don ya horas da su kwallo.

A cewar Ephrem, cikin shekaru da dama, ya yi nasarar horas da yara sama da 100 kwallon kafa. Ya kuma gamsu cewa, yaran Sinawa na da kwazo kwarai da gaske, suna da dagewa wajen cimma burin da suka sanya gaba.

Ya ce "Yaran Sinawa da na hadu da su, sun nuna min irin himmar su ta cimma burin da suka sanya gaba. Don haka, ko shakka babu, harkar kwallo kafa ta Sin, za ta ci gaba da bunkasa sannu a hankali. Ina mafarkin ganin wadannan yara na kwallo a manyan kungiyoyi na duniya, ciki hadda wadanda za su bugawa kasar su. Zan ci gaba da ba da gudummawa domin cikar wannan buri!"