logo

HAUSA

Ya Kamata Mu Ci Gaba Da Raya Kauyuka Domin Karfafa Sakamakon Da Aka Cimma A Fannin Yaki Da Talauci

2020-12-18 15:29:38 CRI

Ya Kamata Mu Ci Gaba Da Raya Kauyuka Domin Karfafa Sakamakon Da Aka Cimma A Fannin Yaki Da Talauci

Kawo yanzu, kasar Sin ta cimma nasarar kawar da dukkanin gundumomi masu fama da talauci daga kangin talauci kafin karshen shekarar bana, wannan shi ne, babbar nasarar da kasar Sin ta samu har ma ta samu yabo daga kasa da kasa.

Amma, bayan kawar da talauci a wasu gundumomin kasar Sin, wasu sabbin matsaloli suke kunno kai, sabo da wasu manoma ba su da karfi sosai wajen fuskantar da kalubaloli na iri-iri, shi ya sa, akwai iyuwar komawarsu cikin talauci. Dangane da hakan, kawar da talauci ba zai iya zama aiki na karshe ba, amma mataki na farko ne cikin sabon aiki na kasar Sin.

A shekarar 2021 mai zuwa, aiki na gaba, shi ne raya kauyuka bisa fannoni daban daban, inda za a yi amfani da dabarun kawar da talauci wajen inganta bunkasuwar kauyuka bisa fannoni da dama, ta yadda za a sa kaimi ga manoma wajen raya harkokin masana’antu da sana’o’i daban daban, domin samun bunkasuwa da wadata.

Bugu da kari, aikin daidaita bambancin dake tsakanin birane da kauyuka shi ne muhimmin aiki dake gabanmu wajen raya kauyuka, kana aiki ne mai wahala dake daukar dogon lokaci. Ba za a cimma burin gina kasa ta zamani bisa dukkan fannoni ba, in babu bunkasuwar yankunan karkara. A don haka, ya kamata mu ci gaba da mai da aikin raya kauyuka da harkokin gona a matsayin babban aikin gina kasa ta zamani, habaka harkokin masana’antu, da kuma neman daidaito tsakanin bunkasuwar birane da kauyuka, ta yadda dukkanin al’ummomin kasar Sin za su samu wadata cikin hadin gwiwa, ta yadda dukkanin mazauna kauyuka za su ji dadin rayuwa. (Maryam Yang)