logo

HAUSA

A tsakiyar huldar dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Nijar

2020-12-18 09:13:14 CRI

A cikin wata hira ta musammun tare da mai girma jakadan kasar Sin a Nijar, mista Zhang Lijun, shugaban diplomasiyyar kasar Sin a Nijar ya gabatarwa masu karanta wata mujallar da ake kira “NIGER INTER” matsayin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma yadda huldar dangantaka ta kasance tsakanin kasar Sin da Nijar.

Da ake tambayarsa yaya halin dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Nijar, mista Zhang Lijun ya amsa da cewa, dangantakar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar jamhuriyyar Nijar ta samu tushe wajen shekarar 1974. Wadannan shekarun baya bayan nan ta dalilin hada karfi da karfe na gwamnatoci da shugabannin kasashen biyu, huldodin diplomasiyya tsakanin Sin da Nijar na ci gaba da karfafa da dorewa kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafa a yau. Huldar mu tana cikin wani kyakkyawan lokaci na tarihinta dake bisa wani babban matsayi.

Na farko, kasashen biyu suna da tunani da tsinkaye da kuma manufofi iri guda. Ta wani bangare muna da muradu iri guda na kawo kyakkyawan sauyi ga kasa da kuma kyautata jin dadin zaman rayuwar al’umma. Kasar Sin ta gabatar da muhimman maradu biyu na karni biyu, (gina wata al’umma ta zamani mai cike da cigaba da wadata ta kowane bangare nan da shekarar 2020, sannan tsara wata kasar gurguzu ta zamani dake samun cigaba mai karfi, ta tsarin demokaradiyya, ta bunkasa al’adun ci gaba da zaman jituwa nan da tsakiyar karni na 21) dukufa aiki wurjanjan domin cimma babban sabon salon a wata sabuwar al’ummar Sinawa da gina wata al’umma mai makoma guda ga duniya. A yayin da gwamnatin Nijar ta kaddamar da tsarin sake farfado da kasar Nijar, na ’yan Nijar su ciyar da ’yan Nijar wato “Initiative 3N” kawar da yunwa nan da shekarar 2023, bisa burin tabbatar da ci gaba mai dorewa da bunkasuwar kasa. Ta wani bangare kuma, bunkasa sauye-sauyen tsarin mulkin duniya domin dunkulewar duniya ta kasance daga dukkan fannoni da kuma amfanawa kawo, shi ne fatanmu tare. Mista Zhang Lijun ya cigaba da cewa kasar Sin kamar kasar Nijar suna maida hankali ga yawaita huldar dangantaka da kuma dunkulewar duniya, kuma suna adawa da dukkan wani bangaranci da nuna son kai. Musamman ma tun lokacin da aka zabi kasar Nijar mamba ba ta dindindin ba a zauren kwamitin tsaro na MDD a farkon wannan shekara da muke ciki, kasashen namu biyu sun karfafa dangantakarsu bisa dandalin kasa da kasa domin kare yanayin zaman lafiya, ci gaban duniya da kuma moriya da muradun ci gaba na kasashen biyu, in ji jakadan kasar Sin a Nijar.

Abu na biyu, kasar na maida muhimmin hankali ga huldar dangantaka. Matakin farko na dangantakar kut da kut kuma ta kai tsaye sannan ta moriyar juna tsakanin kasar Sin da Nijar, da ta shafi taimakawa Nijar samun ci gaba. A yau, Sin ita ce kasa mafi zuba jari, kasa ta farko dake gudanar da ayyuka na jama’a kuma kasa ta biyu abokiyar kasuwanci ta kasar Nijar. Wadannan shekarun baya, kasashen biyu sun cimma nasarar gudanar da ayyuka da dama a fannoni daban daban na makamashi, ma’adinai, manyan gine-gine da kiwon lafiya. Kuma, kasar Sin ta baiwa Nijar taimako da dama domin ci gaban tattalin arzikinta da na al’umma, kawo zuba jari da ma’aikata, da kuma bada kwarin gwiwa ga musanyar fasahohi da kimiyya. A karshe, a matsayin babbar kasa mai karfin ci gaban masana’antu kuma mai fitar da kayayyaki a duniya, kasar Sin ta samarwa al’ummar Nijar da kayayyaki masu inganci kuma a farashi mai rahusa. Darajar karfin kasuwanci tsakanin kasashen biyu sai kara karuwa yake, har ya cimma matsayin koli tare da jimillar dalar Amurka miliyan 511, kimanin wata karuwa ta kashi 77,9 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, cewar mista Zhang Lijun.

Abu na uku, abokantaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu na ci gaba da karfafa. Ta dalilin zurfafar musanya tsakanin al’ummomin kasashen biyu, fahimtar juna ta karfafa. Wadannan shekarun baya bayan nan, dubayen manyan masu kwangiloli da ’yan kasuwa na kasar Nijar na zuwa kasar Sin kowace shekara domin gudanar da harkokin kasuwanci, daruruwan ’yan Nijar da suka fito daga bangarori daban daban sun je kasar Sin domin yin musanya, samun horo ko kuma yin karatu. Wata tawagar gwamnatin Nijar ta kuma halarci baje kolin kasa da kasa na shuke-shuken lambuna ko garake na Changsha na shekarar 2019, tare da gabatar da noma da noma guda na Nijar ga al’ummar Sinawa. Haka kuma, kwana tashi kamfanoni da ’yan kasar Sin suna zuwa Nijar domin zuba jari ko yin yawon bude ido da shakatawa. Abin da ya kamata a jaddada, shi ne al’ummar kasar Sin a Nijar na halarta sosai cikin ayyukan amfanin jama’a domin rakiyar mutanen Nijar wajen jurewa wahalhaloli na matsalolin da ambaliyar ruwa ta janyo, fari da annoba. Al’adun kasar Sin kuma na cigaba da samun karbuwa a Nijar. Misali, ta dalilin hada karfi da karfe na ofishin jakadancin Sin a Nijar da kungiyar wasan Kung-Fu ta kasar Nijar, wasu gasannin wasan Kung-Fu ne aka shirya a tsawon shekaru uku a jere da kuma janyo dubayen masu sha’awar wannan wasan Kung-Fu da kuma ’yan kallo Nijar.

Abu na hudu, kasashen biyu suna nuna tunanin kirkirowa da marama juna. Sin da Nijar suna tallafawa juna koda yaushe musammun ma a lokuta masu wuya da kuma jurewa kalubale tare, kamar abin da ya faru gaban annobar cutar Covid-19 a wannan shekara. A karshen watan Janairu, a lokacin da kasar Sin ta yi fama da yakinta da wannan annoba, shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou da al’ummar Nijar sun kawo muhimmin goyon bayansu da nuna ayyukan zumunci ga kasar Sin, abin da ya bada kwarin gwiwa ga al’ummar Sinawa wajen daure damara wajen yaki da cutar lumfashi ta coronavirus. Alhali, tun lokacin bullowar cutar a Nijar, gwamnatin kasar Sin, ofishin jakadancin Sin a Nijar, da kuma kamfanoni da kungiyoyin kasar Sin sun bada taimakon kayayyakin likitanci magunguna sau da dama da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyin kudin Sefa, da suka kunshi na’urorin lumfashi guda 43, da kayayyakin gwaji kusan dubu 40 da takunkumi kusan miliyan 1.4, baya ga kuma tallafin kudi. Bisa burin rakiyar gwamnatin Nijar wajen fuskantar kalubalen tattalin arziki da na zamantakewa da annobar ta janyo, da sauyin yanayi da kuma matsalar tsaron abinci, gwamnatin kasar Sin ta samar a wannan shekara da wani taimakon abinci wato shinkafa ton dubu 5 da dari 9. Irin wannan taimako shi ne na uku a tsawon shekaru uku na baya bayan nan wanda ya hada a jimilce ton dubu 15. Baya ga wannan akwai karin taimako na ofishin jakadancin kasar Sin a Nijar na kudin Sefa miliyan 15 zuwa ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su, da kuma wani taimakon musamman na darajar kudin Sefa miliyan 55 da ya fito daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, a cewar jakadan kasar Sin dake Nijar, mista Zhang Lijun.

Allah ya kara daukaka huldar dangantaka bisa matsayin koli kuma daga dukkan fannoni tsakanin kasashen Sin da Nijar, kuma da dorewar zumunci da abokantaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu, domin ci gaban kasashen biyu da kuma ci gaban duniya mai zaman lafiya da zaman jituwa bisa girmama juna da cin moriya tare.

Allah ya sanya karin dankon zumunci tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika, sannan kuma tsakanin Sinawa da al’ummomin kasashen Afrika baki daya.

(Fasarar hirar jakadan kasar Sin a Nijar mista Zhang Lijun da harshen faranci zuwa harshen hausa, Mamane Ada daga birnin Yamai zuwa sashen Hausa na rediyon kasar Sin cewa da CRI)