logo

HAUSA

Shaidu da gaskiya game da karyar da ake bazawa kan Xinjiang

2020-12-18 20:16:05 CRI

Shaidu da gaskiya game da karyar da ake bazawa kan Xinjiang

A ranar 15 ga wata, cibiyar nazarin manufofin kasa da kasa, ta masanan Amurka ta fitar da wani rahoto, inda aka yi zargi cewa, ana tilastawa ‘yan kabilar Uygur sama da dubu 500 a jihar Xinjiang yin aikin tsintar auduga na dole, a jiya Alhamis 17 ga wata, majalisar dokokin Turai ta zartas da wani kuduri, inda ta suka gwamnatin kasar Sin kan yadda take tilastawa ‘yan kananan kabilun jihar Xinjiang yin aikin dole.

Hakika wasu ‘yan siyasa wadanda ke yin adawa da kasar Sin suna daukar kokarin gwamnatin kasar Sin na samar da aikin yi ga al’ummun kabilu daban daban na jihar Xinjiang a matsayin tilasta yin aikin dole, domin shafawa kasar Sin bakin fenti, tare kuma da lalata huldar dake tsakanin kabilu daban daban na kasar Sin, da ma hana ci gaban kasar Sin.

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan “samar da aikin yi ga al’ummun jihar Xinjiang”, da “rahoton binciken yanayin da ake ciki a jihar Xinjiang a bangaren samar da aikin yi” da sauran takardu, inda aka yi cikakken bayani kan hakikanin yanayin da ake ciki a jihar, da manufar samar da aikin yi ta jihar wato mutunta ‘yancin samun aikin yi na al’ummun jihar, da tabbatar da hakkin ‘yan kwadago na jihar, da makasudin samar da aikin yi ga al’ummun jihar wato samar musu taimako ta yadda za su yi rayuwa cikin farin ciki.

An lura cewa, a daidai wannan lokacin, da gwamnatin kasar Amurka ta wannan karo ke shirin kammala wa’adin aikinta, wasu ‘yan siyasa na kasar kamar Mike Pompeo suna gurgunta kasar Sin, wannan shi ne dalilin da ya sa aka sake baza karya kan batun Xinjiang.

Game da manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa kan jihar Xinjiang, da ci gaban da aka samu a jihar a bangaren kiyaye hakkin bil Adama, yawancin kasashen duniya sun nuna goyon bayansu, a bayyane an lura cewa, yunkurin wasu ‘yan siyasar kasashen yamma na yin adawa da kasar Sin, ba zai iya goge hakikanan abubuwan dake shafar kwanciyar hankali da wadata da aka samu a jihar Xinjiang ba, ko shakka babu, yunkurinsu na siyasantar da batun Xinjiang da tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin ba zai yi nasara ba.(Jamila)