Dawowar tsagin sauka na tauraron Cheng’e-5 babbar nasara ce da duniyar kimiyya
2020-12-17 19:36:40 CRI
Ga duk mai bibiyar labarai masu nasaba da irin ci gaban da bil Adama ke samu a fannin binciken kimiyya da fasaha, ba zai kasa jin labari mai faran ta rai, na dawowar tsagin sauka na tauraron dan Adam samfurin Cheng’e-5 da kasar ta harba zuwa duniyar wata a karshen watan Nuwamba ba.
Ko da yake ba wannan ne karon farko da wani tauraron dan Adam ya taba gudanar da aiki debo samfuran sinadarai daga duniyar wata ba, amma masana kimiyyar sama jannati sun ce, ayyukan da Cheng’e-5 ya yi a wannan karon a duniyar wata suna da sarkakiya, sun kuma shafi tattaron samfuri daga duniyar wata, ta saukowa da su nan duniyar bil Adama, da ma wasu karin ayyuka masu nasaba da hakan.
Hakika Cheng’e-5 ya kafa tarihi a kasar Sin da duniya baki daya, a fannin nazarin sararin samaniya. Ya zamo wata gada ta sada binciken da aka jima ana yi, da wanda za a yi a nan gaba. Zai kuma baiwa masana ‘yan samajannati karfin gwiwar ci gaba da bincike, da dorawa inda aka tsaya, karkashin manufar kasar Sin ta kafa tashar binciken samaniya mallakin kan ta.
Tuni dai shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jinjinawa wannan aiki, tare da fatan alheri ga daukacin ma’aikata da suka ba da gudummawar kammalar sa cikin nasara.
A hannu guda kuma, la’akari da wannan nasara, kasar Sin ta nunawa duniya irin jajircewar ta, wajen cimma manyan nasarori daga dukkanin fannoni. A wannan gaba da duniya ke fuskantar wahalhalu da kalubale, kuma masana ke kara yayata bukatar komawa ga matakan kimiyya da fasaha wajen warware matsaloli, Sin ta nuna himmar ta a wannan bangare.
Ana sa ran sinadarai da sundukin dawowa na Cheng’e-5 ya zo da su, za su kara haskawa masu bincike yanayin kasa, da sinadarai, da ma tarihin duniyar wata, wanda ilimi ne da duniya ta dade tana kishirwar sa.
Ko shakka ba bu, Bahaushe kan ce “yabon gwani ya zama dole”, kammalar aikin Chang'e-5 zai dade yana tunawa duniyar bil Adama, irin rawar gani da Sin ta kara wajen fadada binciken duniyoyin dake kewaye da duniyar bil Adama, ciki har da duniyar wata, da ma daukacin sassan ayyukan samajannati.