logo

HAUSA

Yaki da talauci a Hetian na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta

2020-12-16 08:58:58 CRI

Kamar dai yadda Bahaushe kan ce, “Gani ya kori ji”, ziyarar gani da ido da muka yi a garin Hetian dake kudu maso yammacin jihar Xinjiang, ta haskaka mana, mu ’yan jarida ’yan kasashen waje, yanayin da wannan yanki mai tarin kabilu daban daban yake, dama irin zamantakewar al’ummunsu a bangarorin raya al’adu, tattalin arziki da ’yancin bin addinai.

Yaki da talauci a Hetian na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta

Wannan ziyara ta ba mu damar ganin irin ci gaba da wannan yanki ya samu, a fannin bunkasar muhimman abubuwan bukatun rayuwa kamar abinci, da kiwon lafiya, tsaro da ilimi tun daga tushe. Mun kuwa san cewa rashin wadannan abubuwa muhimmai, a yawancin lokuta shi ke haifar da gurbacewar rayuwa, da rashin tsaro, da rashin samun ci gaba tsakanin al’umma.

Karkashin manufar kasar Sin ta yaki da talauci, an kafa kamfanoni daban daban, dake samar da guraben ayyukan yi, da koyar da sana’o’i, da kuma yin hadin gwiwa da mazauna yankunan da aka kafa kamfanonin domin yaki da fatara tare.

Cikin manyan misalai kan hakan, akwai yadda aka inganta ginin unguwar Hotan Tuancheng dake Hotan, ta yadda ta zama unguwa mai karbar ’yan yawon shakatawa, wanda ke tururuwar ganin kayayyakin al’adun al’ummar yankin. Kaza lika an samar da kayan more rayuwa a yankunan Hamadar Takla Makan dake wannan yanki, ta yadda Hamadar ta zama mai ban sha’awa, wadda kuma ke jawo ’yan yawon bude ido.

Yaki da talauci a Hetian na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta

A bangare guda kuma, kamfanonin da suka amince su kafa rassan su a wannan yanki, suna samun gata na rangwamen haraji da sauransu, ta yadda zamansu a yankin zai samar da damammaki na guraben ayyukan yi ga mazauna wurin.

A bangaren kiwon lafiya ma, an samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin manya da kananan asibitoci, ta yadda mazauna yankin ke iya ganin kwararrun likitoci a wuraren su na asali, ba tare da sun yi tafiya mai nisa zuwa birane ba.

Yaki da talauci a Hetian na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta

A bangaren damar gudanar da addinai, na ganewa idanu na yadda mabiya addinin musulunci ke gudanar da sallah, a babban masallacin Kuonaxiehai'er dake gundumar Moyu na al'ummar Uygur, da masallacin Jiaman dake yankin Hotan wanda ke da tarihin shekaru 145 da kafuwa.

Muna iya cewa, kafin mutum ya gaskata kafofin dake yada labarun sukar kasar Sin game da harkokin iddinai, da ‘yancin ‘yan kwadago, ya dace ya bibiyi rahotanni na ganau, dake tantance ainihin halin da wannan yanki na Xinjiang ke ciki. (Ibrahim Yaya, Saminu Hassan/Sanusi Chen)